1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Karin kudin fito don bunkasa masana'antu

Mohammad Nasiru Awal
January 5, 2017

A wani mataki na bunkasa masana'antun cikin gida da jawo hankalin 'yan kasa wajen amfani da kayayyakin da ake samarwa a gida, gwamnatin Najeriya ta yi karin kudin shiga da kaya kasar daga ketare.

https://p.dw.com/p/2VKMj
Öl Ölförderung Nigerdelta Niger Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa

Gwamnatin Najeriya ta yi karin kudin fito da wasu kayayyaki na jin dadi da motoci tare da rage kudin da ake biya a kan kayayyakin masana’antu a mataki na taimaka farfado da masana’antu na cikin gida da sanya al’umma amfani da kayayyakin da ake samu a kasar maimakon dogaro da na kasashen waje.