1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damar mallakar bindiga a Najeriya

August 13, 2020

Kasa da 'yan sa'o'i da shawarar gwamnan Benue na halasta  mallakar bindiga a Tarayyar Najeriya da nufin kare kai, muhawara ta barke cikin kasar game da mallakar makaman domin kawo karshen rikici.

https://p.dw.com/p/3gvWx
Nigeria Viehdiebstähle in ländlichen Regionen
Yaduwar makamai a Najeriya, na taka rawa wajen lalacewar al'amuran tsaroHoto: DW/Katrin Gänsler

Tun bayan faduwar gwamnatin Shugaba Mu'ammar Ghaddafi a Libiya dai, yanki na yammacin Afirka ya kalli karuwa ta kanana na makamai da ake tallakawa da karin riginmu a cikinsa. Wani rahoto dai na nuna kashi kusan 70 na makamai kusan miliyan 500 da aka kiyasta na hannu na fararen hula a cikin yankin dai, na cikin Tarayyar Najeriya da ke zaman kasa mafi yawan al'umma sannan kuma ta kan gaba cikin fuskantar rikicin da ake alakantawa da yaduwa ta makaman.

Bazuwar kananan makamai

Karuwa ta makaman dai ce ake ta'allakawa da karuwa ta tashi na hankali walau na Boko Haram a Arewa maso Gabas ko kuma 'yan ina da kisan da suka addabi al'ummar yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya a kasar.

Nigeria Kaduna Strategie gegen Terrorismus
Kaddamar da kungiyar tsaron arewacin NajeriyaHoto: DW/Ibrahima Yakubu

Ko a farkon wannan mako dai jami'an tsaro a Jamhuriyar Nijar sun halaka wasu dillalai na makaman da suke shirin shiga Najeriyar daga Libiya, a wani abun da ke nuna ta'azzarar annobar. To sai dai kuma gazawa ta jami'an tsaro na tunkarar lamura ya kai ga musayar yawu, game da hanyoyin tunkarar matsalar da ta dauki lokaci sannan kuma ke neman wucewa da sanin mahukunta. Na baya-baya cikin muhawarar dai na zaman gwamnan jihar Benue Samuel Ortom da ya nemi gwamnatin kasar ta halasta mallakar bindigogi a tsakani na 'yan kasar da ke da hankali, domin kare kai daga jerin barazanar da ta zama ruwan dare a Najeriyar a halin yanzu. Shawarar kuma da ta jawo muhawara mai zafi cikin kasar da kai yake rabe.

Kokarin kisan al'umma ko kuma kokari na kare 'yan kasa, Tarayyar Najeriyar dai ta dauki lokaci tana kokarin rage bazuwar kananan makaman, tun ma kafin ta'azzarar rigingimun.

Nigeria Bürgerwehr in Zamfara
Matasa 'yan sintiri a ZamfaraHoto: DW/Y. Ibrahim

Kuma a fadar Kabiru Adamu da ke zaman mai sharhi cikin tsaron, kyale makamai a wurin al'ummar na iya barazana ga iko na gwamnatin da yai nisa a cikin rauni yanzu. Mai karfi sai Allah ko kuma barazana ga iko na gwamnati, kusan kaso 90 cikin 100 na masu daukar makaman a cikin Najeriyar dai, na zaman matasan da ke kasa da shekaru 45 da haihuwa. Kuma damar ta makamai dai na iya dauke hankali na matasan da ke da burin girma a cikin halin babu.

Rawar matasa a matsalar tsaro

Ta'annati na matasa da makami dai na sanadiyyar mutuwar dubban al'umma a shekara har a kasashen da ke takama na ci-gaba kamar Amirka. Abun kuma da a cewar Nasir Adhma da ke zaman mashawarci na gwamnatin Najeriyar kan harkokin matasan,  ya sa ake bukatar taka-tsan-tsan kan hanyar mayar da bindigar sandar kiwo a kasar. Shugabannin Najeriyar dai daga dukkan alamu na shirin kama takobi, a cikin hanyar neman kai karshen annobar rashin tsaron da ke neman mamaye daukacin kasar a halin yanzu.