1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Yawan 'yan gudun hijirar Najeriya

May 14, 2019

Sama da 'yan gudun hijira 2,000 ne suka shigo a garin dan Kano da sauran garuruwa na kan iyakar Maradi da Zamfara da sabon birnin Sokoto.

https://p.dw.com/p/3IUTt
Nigeria | Flüchtlingslager in Pulko
Al'ummar jihohin Zamfara da Sokoto na tserewa zuwa NijarHoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

'Yan gudun hijirar dai na isa garuruwan kan iyaka Nijar da Najeriya, irinsu  Dan Kano da Nakuka dan tsira da rayukansu daga barazanar 'yan bindiga da ke cin karensu babu babbaka a yankin. 'Yan gudun hijirar dai sun samu tarbo na karamci daga jama'ar garuruwan da suka sauka, inda aka basu wuraren kwana na wucin gadi. Tuni dai hukumar kula da 'yan gudun hijira reshen jihar ta Maradi suka kai ziyarar gani da ido domin tantance girman matasalar. A fili take dai akwai bukatar kawo agajin gaggawa domin a taimaka musu. Kawo yanzu dai jama'ar garuruwan da 'yan gudun hijirar suka sauka ne ke ci gaba da daukar dawainiyarsu kafin gwamnati da masu hannu da shuni su yunkuro.