Najeriya: Yawan hare-haren Boko Haram a Arewa maso Gabas

Hankulan al'ummomi a jihohin Borno da Yobe sun tashi ganin yadda Boko Haram ke kai hare-hare ba kakkautawa a sansanonin sojoji da kuma garuruwa duk da komawar manyan hafsoshin sojojin Najeriya yankin Arewa maso Gabas.

An yi fatan cewa zuwan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi jihar Borno za a samu sauki hare-hare daga Boko haram amma kullum abin karuwa ya ke yi.
Har wayau gwamnatin Najeriya ta bukaci manyan hafsoshin sojojin kasa da da na sama da su koma da zama a shiyyar Arewa maso Gabashn kasar har sai al’amuran tsaro sun inganta lamarin da masana da masharhanta ke ganin ba zai haifar da komai ba tun da ba karo na farko kenan da gwamnatin ke ba da irin wanna umurni ba.

Bayanai masu kama

Rahotanni masu dangantaka