1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar ba da cikakkiyar kulawa ga 'yan gudun hijira

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
December 4, 2018

Majalisar dokokin Nijar ta rattaba hannu a kan wata sabuwar doka da ke bai wa 'yan gudun hijira na cikin gida cikakkiyar kulawa tare da tilasta wa gwamnatin daukar matakai na kariya ga masu hijirar.

https://p.dw.com/p/39RHr
Afrika - humanitäre Hilfe im Tschadsee-Gebiet
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Dubun dubatar jama'a ne yanzu haka ke cikin wani yanayi na mawuyacin hali sakamakon matsalolin tashe-tashen hankula masu nasaba da yaki da masu tayar da kayar baya da kuma ya tilasta masu kaura daga gidajensu daga wasu yankunan zuwa wasu domin samun mafaka musamman ma a yankunan Diffa da ke fuskantar matsalolin 'yan ta'addan Boko Haram, ko a yankunan Tahoua da Tillabery da ke makwaftaka da arewacin Mali masu fama da matsaloli na tsaro.

Babbar manufar da dokar ta sanya wa gaba da majalisar dokokin kasar Nijar ta jefa kuri'ar amincewa da ita da gagarumin rinjaye, shi ne na samar wa dubban jama'ar da ke cikin hali na tagayyara wata ingantacciyar rayuwa tare da kulawa ta musamman daga gwamnatin kasar maimakon barinsu sake.

Lamidou Harouna Moumouni dan majalisar dokokin jamhuriyar Nijar ne mai wakiltar yankin Diffa da ke cewa:

"Gwamnati za ta yi tsari ta yadda su ma wadannan mutanen 'yan Nijar a taimaka masu su samu walwala, su samu ci da tsaro da kiwon lafiya. Wadannan mutanen sune 'yan gudun hijira na cikin gida."

Kirkiro aikin yi ga 'yan gudun hijira

Niger Binnenflüchtlinge Flüchtlinge Vertriebene Nigeria
Yara a sansanin 'yan gudun hijira na Assaga da ke kusa da DiffaHoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Ko baya ga ilimi da kiwon lafiiya da tsaro, kudurin dokar mai ayoyi kimanin 42 dai ya kuma tilasta wa hukumomin kasar samar wa 'yan gudun hijirar na cikin gida wasu muhimman ayyukan yi domin kauce wa zaman banza inji dan majalisar dokoki Lamidou Moumouni.

"Idan suna son wani aiki doka ta ce gwamnati ita za ta duba wannan domin samar masu da aikin yi, doka ta ce idan ka gudu ka bar dukiyarka kamar shanu to gwamnati za ta nemo su, hakan kuma idan kanti ne ka bari to gwamnati za ta nemo abinka ta kawo maka a inda kake gudun hijira. Idan kuma aka kamaka da takura wa wadanda ke gudun hijira a wuraren da suke ko don kana da iko ko kana sata ko wani abu to doka ta ce dole ne sai an kama ka da shekaru 15 zuwa 30 a gidan yari."

Sai dai duk da yake daukacin 'yan majalisar dokoki na kowane bangare suka sanya hannu ga kudurin dokar da dama daga cikin 'yan rajin kare hakin dan Adam da ma masu sharhi na ci gaba da nuna damuwa dangance da irin yanayin da dokar za ta taka rawa a kai.

Matsalar karancin ruwa na daga cikin matsalolinn 'yan gudun hijira a Nijar
Matsalar karancin ruwa na daga cikin matsalolinn 'yan gudun hijira a NijarHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Shakku kan aiwatar da dokar

Malam Solly Abdoulaye wani mai sharhi ne a kan al'amuran yau da kullum da ya yi tsokaci kan dokar.

"Yau ba ma doka ba, in ka dubi kundin tsarin mulki na kasa akwai ababen da ya tanada da ta kamata a ce gwamnatin ta yi wa talakawa, amma ba ta yi ba to balantana wai wata doka don kula wa da wasu 'yan gudun hijira da sauransu. Gwamnati ba za ta iya ba, daman abin da ya sa suka dauki wannan dokar don su dada rayuwar masu ba su tallafi da ke da wannan fata."

Dokar dai yanzu haka tana a gaban fadar shugaban kasa inda yake da tsawon kwanaki 15 don sanya mata hannu kan ta zamanto doka ta gaskiya.

Ba tun yau ba dai gwamnatin take bayyana daukar matakai na kara inganta rayuwar dubban jama'a da suke fuskantar matsalolin kaura daga gidajensu sakamakon yaki ko matsalolin ambaliya da sauran bala'o'in da ke da nasaba da canjin yanayi.