1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahamane Ousmane yayi fatali da kame kamen yan adawa

Abdoulaye Mamane Amadou
February 28, 2021

Dan takarar jam'iyyar adawa a Jamhuriyar Nijar Mahamane Ousmane, ya bukaci sakin daukacin magoya bayan adawa da ake rike da su ciki har da Hama Amadou.

https://p.dw.com/p/3q1o1
Mahamane Ousman Ex-Präsident Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Mahamane Ousmane da ya ayyana kansa a matsayin wanda yayi nasarar zaben shugaban kasa zagaye na biyu, ya yi fatali da barazanar da yace ake ci gaba da yiwa magoya bayan jam'iyyun adawa, tun bayan barkewar tarzomar bayan zabe da ta yi sanadiyar mutuwar mutun biyu a birnin Yamai.

Ya zuwa yanzu dai ana dakon kotun tsarin mulki ta tabbatar da sakamakon zaben shugaban kasar zagaye na biyu, wanda hukumar zaben CENI ta tabbatar da Mohamed Bazoum a matsayin wanda ya yi nasararsa da kaso 55,75% , sakamakon da madugun adwar Mahamane Ousmane ke ci gaba da karyatawa,