1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa tsakanin shugaban Nijar da kungiyoyin farar hula

Gazali Abdou Tasawa MNA
June 8, 2021

A Jamhuriyar Nijar shugaban kasa Mohamed Bazoum ya gana da shugabannin kungiyoyin farar hula na kasar kan gudunmawar da yake jira daga garesu wajen shawo kan matsalolin da kasar take fama da su.

https://p.dw.com/p/3ub7B
Nigeria I Präsidenten Mohamed Bazoum
Hoto: Facebook/Präsidentschaft der Republik Niger

Wakillan kungiyoyin farar hula sama da 100 ne suka karbi kiran shugaban kasar ta Nijar Mohamed Bazoum inda suka share kusan awoyi uku suna tattaunawa irin na sauke gyara kayanka da bai zamo aje mu raba ba, da ma kuma kan rawar da kungiyoyin farar hula za su iya takawa wajen taimaka wa gwamnatinsa ga shawo kan jerin matsalolin da suka dabaibaye kasar, musamman na cin hanci da rashawa da suka zamo ruwan dare a kasar a shekarun baya bayan nan kamar dai yadda Shugaba Bazoum din ya bayyana a gaban shugabannin kungiyoyin a jawabinsa na share fagen tattaunawar.

"Muna bukatar gudunmawarku a yaki da cin-hanci da rashawa, ina so ku taimaka mani ga fallasa asirin duk wasu masu miyagun dabi'u da suka tauye Nijar tsawon shekaru wadanda a baya mun yi ta yakarsu amma ba mu gamsu da sakamakon da kokowar tamu ta bayar ba. Don haka daga yanzu ina son mu yi hulda ta mutunci da fada wa juna gaskiya, wacce za ta taimaka mana ga shimfida mulki na adalci. Kuma ba na yi maku wannan tayi ba ne don neman suna ko don in burge ku ko don in yaudari al'umma, na yi ne tsakani da Allah don in samu goyon bayanku, don ganin bayan duk wasu baragurbi wadanda suka gurbatar da ma'aikatunmu."

Tun ba yau ba gwamnatin Nijar ta kaddamar da yekuwar yaki da cin hanci da rashawa
Tun ba yau ba gwamnatin Nijar ta kaddamar da yekuwar yaki da cin hanci da rashawa

Wannan dai shi ne karo na farko da wani shugaban Nijar ya taba shirya taro da ya hada illahirin kungiyoyin farar hula na kasar har ma wadanda suka kwashe shekaru suna zaman doya da man ja da gwamnatin da ta gabata, kamar su kungiyar Sauvons Le Niger. Kuma shugaban kungiyar Maicon Zodi ya bayyana yadda suka kalli haduwar tasu da kuma abin da suke jira daga shugaban kasar.

Karin bayani: Nijar: Kokarin shawo kan matsalar tsaro

"Mun saurare shi ya ce mu kama mishi zai yi yaki da cin hanci da rashawa, zai yi aiki da dokokin kasa, zai yi aiki 'yan Nijar su ji dadi cikin kasarmu. Mu mika shi takarda mai kunshe da irin matsalolin Nijar da abin da muke son ya yi wa 'yan Nijar. In ya yi wannan bukatarmu ta biya. Zai ganmu muna kama mishi, in kuma bai yi ba to dama mun saba gwagwarmaya, za mu fito mu nuna mishi kurenshi."

Ita ma dai Samira Sabou shugabar kungiyar Bloger ta masu fafutika a shafukan sada zumunta wacce ta sha dauri a gwamnatin da ta gabata, ta kasance a taron tattaunawar da shugaban kasa, ta kuma ce kalaman shugaban kasar sun sosa mata rai sosai, amma suna bukatar gani a aikace.

Karin bayani: Shugaban Chadi Mahamat ya ziyarci Bazoum

A karshen tattaunawar tasu dai Shugaba Mohamed Bazoum ya bayyana bukatar shirya irin wannan haduwa lokaci zuwa lokaci da kungiyoyin farar hula domin ci gaba da fitar da shawarwari na gano bakin zaren warware matsalolin kasar ta Nijar domin kuwa 'yan magana na cewa idan dai har baki na gamuwa to kuwa rai ba ya baci.