1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Gargadin MDD kan ambaliyar ruwa

Gazali Abdou TasawaMay 31, 2016

Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya wato Ocha ta ce 'yan Nijar sama da dubu 100 na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a daminar wannan shekara ta 2016.

https://p.dw.com/p/1IxnA
Mosambik Überflutung
Hoto: picture-alliance/dpa

Majalisa Dinkin Duniya ta ce akwai yiwuwar a wannan shekara ta 2016 Nijar ta fuskanci mummunar ambaliyar ruwa da ka iya shafar rayuwar mutane sama da dubu 100 a garuruwan da dama na kasar wacce ke daya daga cikin mafi talauci a duniya.

A cikin rahotonta na wata wata da ta fitar a wannan Talata, hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya wato OCHA reshen birnin Yamai, ta ce za ta kaddamar da wani shiri na rigakafi da zaran ta lura lamarin ya kai ga shafar kashi biyar zuwa 10 na al'ummar kasar.

Hukumar ta OCHA ta ci gaba da cewa tuni ma dai ta fara daukar matakan soma tattara kudade da kayayyakin bukata ga mutanen da bala'in ka iya ritsawa da su.

A share daya kuma hukumomin kasar ta Nijar sun kaddamar da aikin gina makarin ruwa a gabar kogin Niger domin kare al'umma mazauna gabar kogin na birnin Yamai daga ambaliyar kogin wacce a ko wace shekara ke haddasa asarar rayuka mutane da dabbobi da gidaje da kuma kadarori.