1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Korafin 'yan adawa kan rijistar zabe a Nijar

Mahaman Kanta GAT
May 27, 2020

'Yan adawa a Jamhuriyar Nijar sun zargi hukumar zaben kasar da yinkurin manakisa ga sabon rijistar masu zabe ta hanyar zaftare sunayen wasu mutane daga cikin sabon girgam din masu zaben.

https://p.dw.com/p/3cr0s
Niger Niamey Präsidentschaftswahl Plakat Wahlkommission CENI
Hoto: DW/K. Gänsler

Bayan da annobar Coronavirus ta yi dalilin dakatar da aikin rijistar masu zabe a birnin Yamai da kewaye, a yanzu hukumar zaben kasar ta koma fagen aikin nata domin kammala shi a cikin wa'adin makonni biyu. To sai dai kuma wasu jam'iyyun adawa na kasar ta Nijar sun zargi hukumar zaben kasar wato CENI da zaftare sunayen mutane da dama daga cikin rijistar da aka yi. Malam Ibrahim Yacouba shugaban Jam'iyyar adawa ta MPN Kishin Kasa na daga cikin masu wannan korafi:

Ya ce "Ni ganau ne ba jiyau ba. Muna da misalai masu yawa na garuruwan da matsalar ta faru inda alal misali akwai garin da aka yi rijistar mutun 900 amma kuma da hukumar zaben ta wallafa sunaye mutun 49 kadai suka ga sunansu daga cikin mutanen garin. Akwai garin da aka yi rijistar mutane sama da 660 amma da aka wallafa mutane 400 da 'yan kai ne ke kan rijistar, wato an fidda sunayen mutane wajen 241."

Niger Ibrahim Yacouba
Ibrahim Yacouba shugaban jam'iyyar adawa ta MPN Kishin kasaHoto: DW/Abdoulaye Mamane Amadou

Sai dai da take mayar da martani kan wannan zargi, hukumar zaben kasar ta bakin Madame Katambe Mariama mataimakiyar shugban hukumar zaben ta ce zargin ba shi da tushe:

Ta ce " Ka san jita-jita ba mu iya hana ta. Amma mu jami'an hukumar zabe ba ma siyasa. Kuma duk wanda ke son samun cikakken labari kan abin da bai fahimta ba, ya zo cibiyarmu mu sanar da shi. Kuma babu wani boye-boye a cikin aikin rijistar masu zaben da gyaranta. Sannun mutane da dama da ba a yi rijistar su ba makiyaya ne da ba a iske su ba a gida a lokacin aikin rijistar. Kenan ko an ga wasu kurakurai ba laifin hukumar zabe ba ne."

Yanzu haka dai 'yan adawar kasar na ci gaba da kaurace wa kujerunsa a hukumar zaben kasar. Sai dai sun ce ala kulli halin za su shiga zabukan da ke tafe.