1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Malaman kwantaragi sun koka kan albashi

Mahaman Kanta
January 14, 2022

A jamhuriyar Nijar malaman makaranta sun ja zare da hukumomi kan rashin samun albashi a kan kari kamar sauran ma'aikata.

https://p.dw.com/p/45Yra
Wasu yara yan makarantar firamare a cikin aji
Hoto: Luc Gnago/REUTERS

Wannan matsala ta malamai 'yan kwantiragi dai, ta jima ta na janyo cece-kuce a Jamhuriyar ta Nijar. Matsalolin dai suan hadar da biyansu albashin da bai taka kara ya karya ba, kana kuma akan biya su albashin a makare ba tare da sauran abokan aikinsu na din-din-din ba duk da cewa sune ke da kaso sama da 70 cikin dari na adadin malaman makarantun firamare da na gaba da firamare a Jamhuriyar ta Nijar.

Koda yake a yayin rantsar da shi, Shugaba Mohamed Bazoum da shi ma ya kasance tsohon malamin makaranta a Jamhuriyar ta Nijar, ya sha alawashin shawo kan matsalolin da ilimi ke fuskanta a kasar ciki kuwa har da alkawarin da ya dauka na mayar da malaman kwantiragin zuwa na din-din-din.

Sai dai har kawo yanzu ba a kai ga cika musu wannan buri nasu ba, koda yake mahukuntan sun nunar da cewa suna sane kuma suna daukar matakan da ya dace domin shawo kan matsalar.