1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen masana dokoki a Nijar

Gazali Abdou Tasawa LMJ
October 6, 2020

A Jamhuriyar Nijar kungiyar masana dokokin tsarin mulki sun nuna damuwa dangane da yadda wasu 'yan siyasa ke yi musu barazana a game da fashin baki da suke yi kan dokar zabe.

https://p.dw.com/p/3jVMY
Verfassungsgericht in Niamey Niger
Masana dokoki a Jamhuriyar Nijar, na zargin 'yan siyasa da yi musu barazanaHoto: DW/M. Kanta

Kungiyar masana dokokin tsarin mulkin na Jamhuriyar Nijar dai, ta nunar da cewa sau da dama fashin bakin da 'ya'yanta ke yi kan dokar zabe da ke nuni da tarnakin da takardun wasu 'yan takarar ka iya fuskanta a gaban kotun tsarin mulki, na janyo musu barazana daga 'yan siyasar. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin kare dimukuradiyya ke nuna fargaba a game da zafafan kalamai da ke fita daga bakunan wasu 'yan siyasar kasar a wannan lokaci.

Karin Bayani: Hama ya yi taron gangami a Maradi

Ko da shi ke cewa kungiyar masana dokokin tsarin mulkin kasar ta Nijar, ba ta fito fili ta zargi wata jam'iyya ko kuma wani dan siyasa game da wannan barazana da mambobinta suke fuskanta ba, amma dai ta ce a zahiri ta ke cewa suna fuskantar barazana har ma da ta kisa daga wasu magoya bayan 'yan siyasa a duk lokacin da wani daga cikin mambobinta ya yi fashin baki kan dokokin zabe musamman kan matsalar da ke tattare da takarar wasu 'yan siyasa a zaben shubana kasar da ke tafe. 

Niger Wahlkampf - Anhänger der Opposition
Kalaman tunzura yayin yakin neman zabe a NijarHoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da yanzu haka ake fuskantar zafafan kalamai daga bakunan wasu 'yan siyasar, inda ta kai wani daga cikinsu na kira ga magoya bayansa da su dauki doka a hannunsu ta hanyar kona mutum a duk lokacin da za a yi musu magudin zabe  a zabukan da ke tafen. Kalamam da suka soma tayar da hankalin 'yan kasa da masu fafutukar kare dimukuradiyya a Nijar din. 

Karin Byani: Shirin zabe da rudanin siyasa a Nijar

A nasa bangaren, Malam Son Allah Dambaji wani dan fafutukar kare dimukuradiyya a Nijar din, kira ya yi ga shugaban kasa Mahamadou Issoufou da ya gaggauta daukar matakin saita 'yan siyasar tun da wuri, kafin su kai ga jefa kasar cikin halin rudani. 

Karin Bayani: Dambarwa kan dokar tsawaita wa'adin kananan hukumomi 

Yanzu haka dai, tun kafin a shiga yakin neman zaben a Jamhuriyar ta Nijar, kowace rana zafafan kalamai ne na kabilanci da bangaranci ke fita daga bakunan wasu shugabannin siyasar kasar ta kafafen yada labarai, a yayin da magoya bayansu ke ci gaba da cin mutumcin juna a shafukan sada zumunta ba tare da mahukunta sun dauki mataki a kai ba.