1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Takadama kan dokar zabe

Abdoulaye Mamane Amadou MNA/UIU
November 27, 2018

Takaddama tsakanin 'yan siyasa da hukumar zabe game da batun kidayar jama’ar da suka cancanci shiga kundin rajistar sunayen masu zabe.

https://p.dw.com/p/390ON
Niger Präsidentschaftswahl Ergebnisse
Hoto: DW/K. Gänsler

Sabuwar takaddama ce ta barke tsakanin 'yan siyasar adawa da hukumar zabe game dangane da aikin kidayar jama'a wadanda suka cancanci zabe kuma ba su da takardun da hukumar zaben kasar wato CENI tare da hadin gwiwar da ma'aikatar shari'a suka kaddamar a makwannin baya.

'Yan adawar na zargin hukumomin da wuce gona da iri da kuma yunkurin samar wa jam''yyar da ke mulki wani kundin rajistar sunayen masu zaben don assasa magudi.

Kawo yanzu dai fiye da mutun miliyan hudu ne ba su da takardun haihuwa, amma gangamin da hukumar zabe da ma'aikatar shari'a da ta cikin gida suka yi ya kai ga samar da takardun haihuwa. Wannan wani yunkuri ne da hukumomin kasar ke da shi na samar da wani sabon kundin rajistar sunayen masu zabe na ainihi da ke burin sanya daukacin 'yan kasar da cikakkun bayyanai na cancantar kada kuri'a a zabubbukan da ke tafe.

Takaddama kan batun kundin rajistar zabe

To amma sai dai a yayin da alkaluman hukumomin ke shan yabo da guda daga hukumar zabe, wata sabuwar takaddama ta soma tasowa game da batun tsakanin 'yan siyasa daga bangaren adawa wanda har ma ta kai 'yan adawar sun yi kira ga magoya bayansu da su kaurace wa karbar takardun da ake bayarwa a karkara suna masu zargin hukumomin kasar musamman ma hukumar zabe ta CENI da aikata laifuka a cikin tafiyar.

'Yan adawa a Nijar sun sha yin gangamin sukar lamirin hukumar zabe ta CENI
'Yan adawa a Nijar sun sha yin gangamin sukar lamirin hukumar zabe ta CENIHoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Malam Annabo Soumaila kakakin kawancen jam'iyyun adawar na FRDDR, ya ce su waye a Nijar wadanda ba su da takardun haihuwa. Duk wadanda suke da takardun haihuwa a Nijar duk an san da su: Ya ce duk dabara ce kawai kuma mun gane ta yadda za su je su dauki mutane da yawa su rubuta kai tsaye da an je zabe sai a ce sun ci zabe, "mun ce mutanenmu da su kaurace ka da su fito a rubuta sunansu kuma ya kamata wannan aikin tun kafin dare ya yi su barshi saboda muna da labarin wadanda aka rubuta har da 'yan shekara biyu ma da haihuwa."

'Yan adawar dai na zargin hukumomin kasar da neman samun wasu hanyoyin da ma wani sabon salo da za su iya kai wa ga jam'iyyun da ke mulkin kasar markayewa a kan madafun iko. Dalilan da ya sa suka sanya gwamnatin kenan ta shirya duk wasu batutuwan da ke da nasaba da kawo gyaran fuska ga sha'anin zabe kuma suke haifar da tarnaki inji kawancen na 'yan adawa.

Take-taken yin magudin zabe

Kakakin kawancen 'yan adawar ya ce wannan gwamnatin ba su yarda da ita ba, mugun nufi gareta, ba sa son barin mulkin don shi ne suke ta wasu kwane-kwane ga zabe suna son batar da mutane kawai domin ba sa son a yi zabe na tsakani da Allah.

Sai dai duk kokarin da DW ta yi domin jin ta bakin hukumomin da yanzu haka tawagoginsu ke cikin karkara don samun martani ciki har da hukumar zabe hakar mu ba ta cimma ruwa ba. To amma a can baya a yayin wani taron manema labaru da shugaban hukumar zabe ya kira Issaka Sounna ya bayyana cewar ko da hukumar zabe ko babu ita wajibi ne ga hukumomin kasar su samar da cikakkun takardu na haihuwa ga 'yan kasar. Saboda haka bai ga dalilin da zai sanya hukumar wadda ke tunkarar zabubukan da ke tafe kauracewa batun ba, domin kuwa babban burin hukumar shi ne na samun dimbin 'yan kasar da suka cancanci zabe sun kada kuri'a a yunkurinta na shirya zabe na gaskiya.

UN-Klimakonferenz 2017 in Bonn | Mahamadou Issoufou, Präsident Niger
Shugaban Nijar Mahamadou IssoufouHoto: Getty Images/AFP/P. Stollarz

A martanin da ta mayar game da sabuwar takaddamar, jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulkin kasar cewa ta yi duk korafe-korafen da 'yan adawar ke yi wani sabon salo ne kawai na guje wa zabubbukan da ke tafe inji Malam Assoumana Mahamadou kakakin jam'iyyar ta PNDS Tarayya. Ya kara da cewa 'yan adawar sun rude ne kawai.

Wannan sabon rikicin da kuma  batun aikin mallakar takardun haihuwa da 'yan siyasar adawa ke yi da gwamnati na zuwa ne a yayin da duk wani batu na sulhu game da batun kundin tsarin zaben kasar  ya tsaya cak tsakanin bangarorin siyasar kasar. Hakan na kuma matsayin wani sabon babi na wani kiki-kaka game da batutuwan zaben da ke shirin kunno kai a shekara ta 2020.