Matashiya mai sana'ar dinka riguna a Nijar
November 20, 2019Talla
Matashiyar dai Salamatou Boubacar mai shekaru 33 da haifuwa ta yi karatunta ne a jami'a inda ta karanci fanin lisafi. Sai dai ganin cewar ba ta samu aiki ba na gwamnatin hakan ya sa ta yi tunanin kirkiro nata kamfanin, wanda ya kunshi ma'aikata da dama da ke a karkashinta suna aiki. Kamfanin yana aikin buga katunan aure ko suna da kuma riguna wanda takan sayar da su a bisa kasuwanni. Babban tallafi da kamfanin na Salamatou ke bai wa matasa shi ne horo ga wadanda da suke da sha'awar bude nasu kamfanin.