1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar na martanin kashe sojan Amirka

Abdul-raheem Hassan
October 5, 2017

Al'umma a NIjar na tofa albarkacin bakinsu dangane da harin da ya kashe sojojin Amirka uku da na Nijar a arewacin jahar Tillabery, harin shi ne na farko ga sojojin da ke yammacin kasar mai makwaftaka da arewacin Mali.

https://p.dw.com/p/2lGxs
Mali Anschlag in Gao
Hoto: Getty Images/AFP

Har yanzu hukumomin jamhuriyar Nijar ba su bayyana wata takamaimiyar sanarwa dangane da harin kwantar baunar da ya auku a yammacin kasar kan sojojin ba, amma rahotanni sun tabbatar da cewar harin ya auku ne a garin Tongo-Tongo wani kauyen mai tazarar kilo mita akalla 80 da garin Oualam mai nisan kilo mita 100 a yamma maso arewacin birnin Yamai.

Da yake hira da tashar DW, dan majalisar dokokin yankin da aka kai harin Honorable Boureima Karimou, ya ce maharan sun fito ne daga yankin Arewacin Mali dauke da bindigogi a cikin motoci da babura inda suka sammaci ayararin sojan hadin gwiwar kasar Nijar da na Amirka da ke sintiri a yankin,

Nigeria Soldaten Archiv 2013
Sojoji a bakin aikiHoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

"Mu dai tun da misalin karfe 11 na rana muka samu labarin kai harin inda sojoji na tsaye a garin suna gaida mutane jim kadan bayan sun daga sai maharan suka kai musu farmaki, kawo yanzu labarin da muka samu shi ne sojan Amirka uku sun mutu daya yaji rauni a ya yinda sojan Nijar biyu suka mutu, maharan sun tafi da motoci uku."

Dan majalisar yaci gaba da cewar ya zuwa yanzu ba wani farar hula da hadarin ya ritsa da shi, sai dai gumurzun sojan da yan ta'adda ya yi sanadiyar konewar wata makarantar boko da ke wajen garin, tare da halaka tarin dabbobin jama'a.

""Yanzu hakan kwanciyar hankali ya dawo a garin kuma akwai sojan kasar a ko ina don tabbatar da tsaro, kamar soja 300 ne ke girke a ya yin da jiragen yaki suma ke ajiye sai dai ga alama suma maharani sun kwashe nasu jama'ar da suka mutu don komawa da su kuma sun nufi Mali ne "

Afrika Niger - Von der Leyen mit Kalla Moutari
Malam Kalla Moutary yana tare da Ursula von der LeyenHoto: picture-alliance/dpa/B. Pedersen

Ministan tsaro a Nijar Malam Kalla Moutary, ya tabbatarwa DW da faruwar harin sai dai yaki ya bayyana adadin hasarar rayuka da bangaren gwamnatin Nijar ta yi a ya yin farmakin. Sai dai ya ce gwamnati zata bayar da cikakken sakamako idan majalisar koli ta tsaron kasar ta yi wani zaman taronta na musamman dangance da abinda ya auku a yankin na Tillabery.

Shugaban kwamitin tsaro na majalisar dokoki honorable Hamma Assah, yace dole ne sai jama'a sun yi taka tsantsan domin jiran cikakken sakamako daga hukumomin kasar musamman ma na jami'an tsaron da ke fagen daga a yanzu.

"Akwai sojojin kasa da na sama suna fagen daga kenan, yakamata a tsaya sai idan har sun kamalla tattara bayyanai kafin a samu cikakkun bayanai."

Protest gegen Boko Haram in Niamey, Niger
Hoto: AFP/Getty Images/B. Hama

Tuni kungiyoyin kare hakin dan adam suka fara bayyana nasu ra'ayi dangane da kazamin harin da ya ritsa da sojojin Amirka ba, Laouali Adamou na daga cikin kungiyoyin fararen hulla a Nijar.

"Idan har kayan aiki ne babu to sai a gaya mana, idan kuma wani abu ne ke faruwa sai a fito fili a fada, ba zamu yarda ana kashe mutanen mu ba."

Wannan harin dai na zuwa ne a ya yin da Nijar da sauran kasashen da ke makwaftaka da Mali ke shirin kaddamar da wata rundunar soja da zata yaki aiyukan yan ta'adda, da kuma ke shirin soma aiki a karshen wannan watan. Sai dai kudaden da kasashen ke bukata na G5 sahel sun haura miliyan 450 ko wace shekara, lamarin da ya haifar da shakku ga manyan kasashe ciki har da Amirka. An dai shafe tsawon lokaci da dama ba a samu harin yan ta'adda da ya ritsa da sojan Amirka da ke girke a Nijar.