1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar na yin tankade da rairaya bisa ta'ddanci

Usman Shehu UsmanFebruary 17, 2015

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kama mutane sama da 160 wadanda ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne, bayan hare-haren da kungiyar ta kai a Diffa

https://p.dw.com/p/1Echi
Niger Anti Charlie Hebdo Protest Polizeieinsatz 18.01.2015
Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

Nijar dai ta shiga rundunar hadaka tare da Kamarun da Chadi, don kawar da mayakan kungiyar Boko Haram, inda ita kuwa kungiyar Boko Haram ta maida martani da kai wa dukkan kasashen hare-hare. A Najeriya ma dai sojojin kasar sun sanar kame garin Munguno a jiya Litinin, sai dai fa 'yan Boko Haram sun kaddamar da hari cikin kasar Kamarun, inda suka hallaka sojojin Kamaru biyar.