1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Fargabar yin adalci a shari'ar kotun soji ta Nijar

Gazali Abdou Tasawa ZUD
May 19, 2022

A Nijar, an shiga kwana na uku a ci gaba da shari’ar yunkurin juyin mulkin shekara ta 2018. Sai dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun bukaci sojojin da ke shari'ar su bai wa wadanda ake zargi damar daukar lauyoyi.

https://p.dw.com/p/4BZt2
Niger Symbolbild Fahne | Mahamadou Issoufou
Hoto: Boureima Hama/AFP

A zaman farko na kotun a bana, wanda zai dauki mako daya, kotun shari’ar sojojin ta Nijar, za ta gudanar da shari’u 13 da suka hada da aikata manyan laifuka. Cikinsu har da ta marigayi Kanal Zanguina wanda ake zargi da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin Mahamadou Issoufou ashekara ta 2018, da kuma batun fyade da ake zargin wani soja da aikata wa wata yarinya ‘yan shekara 14. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta ROAD ta bakin shugabanta Malam Son Allah Dambaji ta yi fatan yin adalci a cikin shari’ar.

Shi ko Malam Tahirou Guimba shugaban jam’iyyar 'Model Ma’aikata' tunatarwa ya yi a game da bukatar gurfanar da duk sojin da ake zargi da yunkurin juyin mulki kafin daukar  matakin korar sa daga aiki kamar yadda aka gani a baya-bayan nan a Nijar.
 

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam da dama dai sun yi ta kiraye-kirayen ganin kotun sojojin ta bai wa mutanen da take yi wa shari’a damar daukar lauyan da zai kare su. Sai dai mai shari’a Alio Daouda, shugaban kotun sojojin ya ce babu wani abun fargaba. A cewarsa ''Duk da cewa alkalan kotun sojin ba farar hula ba ne, kotu ce mai kiyaye doka da oda da duk wasu ka’idoji na dokokin kasa.'' Shugaban kotun sojin ya kuma ce idan ma har wanda ake zargi ba shi da lauya, ya zama dole ga kotun ta samar mashi da lauyan da zai kare shi.