1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Hukumar yaci da cin hanci za ta saka ido a zabe

Gazali Abdou Tasawa AH
December 9, 2020

A Jamhuriyar Nijar hukumar yaki da cin hanci da karpar rashawa HALCIA ta sanar da shirin shiga harkokin zabe da ake shirin gudanarwa domin yakar al’adar cin hanci da rashawa a cikin harkokin zabe a kasar.

https://p.dw.com/p/3mToY
Niger Hamdoullaye Wählerinnen
Hoto: DW/M. Kanta

HALCIA ta sanar da haka ne a bikin raya ranar yaki da cin hanci ta duniya(09-12-20) da ta shirya a birnin Yamai, inda ta kuma bayyana sakamakon aikin yaki da cin hanci da ta yi a wannan shekara ta 2020. Wannan dai shi ne karo na farko a Jamhuriyar ta Nijar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar wato HALCIA ta yanke shawarar shiga a hakumance a dama da ita a cikin harkokin zaben kasar. A ranar 27 ga wannan wata na Disamba ne za a gudanar da zabukan gama gari na Nijar.

HALCIA ta sha alwashin yaki da cin hanci ta hanyar bayar da kudade a zaben Nijar

Niger Anti-Korruptionsinitiativen

A lokacin da take yi karin bayyani a kan batun kakakin hukumar uwargida Amadou Zara Idrissa ta ce hukumar ta ce za ta yi maganin cin hanci ta hanyar bayar da kudade a zaben na Nijar. Hukumar ta HALCIA ta sanar da kafa hukuma ta sa ido a harkokin zabe, da kuma bayar da horo ga jami’an hukumar zabe kan dubarun yaki da cin hanci a runfunan zabe. Hukumar ta HALCIA ta sanar da wannan aniya ce ta shiga zaben a wajen bikin raya ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya inda kuma ta bayyana irin nasarorin da ta samu a fannin yaki da cin hanci a tsawon wannan shekara ta 2020 a Nijar. A baya dai rawar da hukumar ta HALCIA  ta taka wajen shirya jarabawa a Nijar ta taimaka ga shirya jarabawa dabam.dabam a cikin tsafta. Abin jira a gani a nan gaba shi ne tasirin da shigar ta a harkokin zaben zai yi.