1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Panama Papers: Badakalar kaurace wa biyan haraji

Mohammad Nasiru AwalApril 7, 2016

Badakalar kin biyan haraji na wasu shugabanni da 'yan kasuwa da ake wa lakabi da Panama Papers na ci gaba da girgiza manyan kasashe da dama na duniya.

https://p.dw.com/p/1IRT5
Symbolbild Panama Papers Mossack Fonseca
Hoto: picture-alliance/maxppp/J. Pelaez

Babbar kungiyar 'yan jaridu ta duniya masu bincike wato ICIJ ta wallafa sakamakon binciken da ta aiwatar, wanda kuma ya shafi manya-manyan mutane har da shugabannin kasashe akalla 12 inda shida daga cikinsu ke bisa mulki da kuma wadanda suka yi suna a fannin wasannin motsa jiki, da ke kaurace wa biyan haraji.