1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ra'ayoyi sun banbanta kan yawan ministoci a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou/USUApril 12, 2016

An nada sabuwar majalisa zartaswa me ministocin 38 a kasar inda a yanzu aka samu karin fiye da ko wane lokaci. Lamarin da masana da wasu 'yan Nijar ke cewa bai dace ba ga kasa da ke fama da talauci.

https://p.dw.com/p/1IU1r
Niger Amtseid des neu gewählten Präsidenten Mahamadou Issoufou
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Daga cikin membobin majalisar ministoci 38 har da 'yan takara uku da suka fafata da shugaba Mahamadou Issoufou a zaben shugaban kasa. Manazarta da kungiyoyin farar hula da ma talakawan kasar ta Nijar na bayyana ra’ayi inda wasu ke ganin majalisar ta yi yawa, a yayin da wasu kuwa ke yabawa. Wadannan su ne ra'ayoyin wasu yan kasar a hirarsu da tashar DW

"Ubangiji Allah ya sa wannan gwamnatin da aka yi ta kasance mafi alkhairi a garemu, tunda anan Bahaushe ya ce ashata yanda aka damata"

Shi kuwa wannan cewa ya yi, "Ministoci Arba’in ba biyu kenan, biyu suka karu bisa ga na farko a ganina yayi yawa"

Haka dai shi ma wannan dan kasar ta Nijar yace "Sunyi yawa fisabilillahi, amma tunda an riga an yi yakamata su tsaya su yi wa kasar ga aiki"

. Itama wannan matar ta yi tsokaci tana mai bayyana ra'ayinta kamar haka. "Gaskiya sun yi yawa akalla dai 20 ko, kamar yadda kasar nan take kuma duk da matsayin da aka baiwa mata mu bai yi ba, ba muyi marhabin da shi ba"

Tuni suma masu sharhin kan al’amuran siyasa suka bi sahun wasu talakawan kasar don nuna damuwarsu kan karin adadin ministocin da ke cikin gwamnatin, tare da cewar hukumomin kolin kasar sun yi kunnen kashi dangance da kiraye-kirayen da suka sha yi, kafin sabuwar majalisar ta bayyana. Alhaji Idi Abdou wani mai sharhi ne a kan al’amuran yau da kullum.

Brigi Rafini , Ministerpräsident Niger 2012
Brigi Rafini,Firaminista kana shugaban majalisar ministocin NijarHoto: Getty Images


"Gwamnati me minitoci da yawa da wuya ayi abin sirri, domin idan ana son a yi abinda ake son cin riba akai. Minista 20 idan ka yi shi daidai da daidai ya yi, babu wani minista wai ministan "Gari" miye minstan gari? kai a naka lissafi me gari a garin da babu magajin gari ne"?

Sai dai tuni sabbin ministocin suka fara mayar da martani kan yawan adadin majalisar ministocin da ta fara shan suka daga wasu manazarta da ma wasu talakawan kasar. Malam Kalla Moutari sabon ministan kiwon lafiyar Nijar ne, a sabuwar gwamnatin.

"Kasan aiki ya yi wa kasar nan yawa. Ana cikin yi amma har yanzu ba’a ida ba, kamar yadda shugaban kasar ke cewa dambu ne ya yi yawa baya jin mai . Dole duk dan kasar da ke iya aiki a kirashi ya zo ya yi, ko wane ofishin minista a shekara sai an yi bincike so biyu"

Sabuwar majalisar dai tuni ta yi wata ganawa ta musamman da shugaban kasa Mahamadou Issoufou, inda ya yi masu jan hankali da tayasu murna dangance da sabbin mukamen nasu.