1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yancin kada kuri'a a Jamus ga mata

Kira Schacht ZMA/LMJ
March 8, 2024

Sama da shekaru 100 ke nan tun bayan da masu ra'ayin mazan jiya na Jamus suka bai wa mata damar kada kuri'a. Hakan ya faru ne a cikin shekarar 1918, a zamanin Jamhuriyar Weimar a Jamus.

https://p.dw.com/p/4dK5S
Jamus | Ranar Mata ta Duniya | 'Yanci | Zabe
Ranar mata ta duniya: 'Yancin mata na fara yin zabe a Jamus

Matan dai sun samu 'yancin shiga zabe a JAmus, bayan yakin duniya na biyu. Zabin jam'iyyu a bangaren matan dai ya canza sosai tun bayan zaben 'yan majalisar dokokin Jamus na farko bayan yakin, wanda a wancan lokacin aka gudanar a Jamus ta Yamma kawai. Tsawon shekaru da dama, jam'iyyar Christian Democratic Union (CDU) mai ra'ayin mazan jiya ta tsohuwar shugabar gwamnati Angela Merkel ta fi shahara a tsakanin mata fiye da maza. A shekarun 1950 da 1960, fiye da rabin mata masu kada kuri'a ne suka zabi jam'iyyar. Elke Wiechmann wanda ya yi bincike kan wakilcin mata a harkokin siyasa a jami'ar Hagen, ya ce wannan matsayi ba zai rasa nasaba da kasancewar jam'iyyar mai mayar da hankali kan kimar addinin Kirista da  da mutunta iyali ba.

Karin Bayani: Jamus: CDU ta sami karin tagomashi bayan zaben jihar Saxony-Anhalt

A wata hira da tashar DW ta yi da shi Wiechmann ya ce sannu a hankali lamarin ya fara sauyawa, tun da aka daina mayar da hankali kan mata. Akwai dai tunanin cewar mai yiwuwa Angela Merkel ta bai wa jam'iyyar CDU karin mata, duk kuwa da manufofin jam'iyyar. Wannan yanayin dai, ya kawo karshe daidai da karewar zamanin mulkin na Merkel. Lokacin da Merkel ba ta sake tsayawa takara ba a zabukan 2021 na baya-bayan nan, jam'iyyar CDU ta sha kaye saboda asarar mata masu kada kuri'a. A cewar manazarta dai, hangen nesan mata daban yake da na maza.

Najeriya: Bikin Ranar Mata ta Duniya

Ga misali mace za ta zabi inganta harkokin sufuri maimakon a gina manyan hanyoyin mota, hakan na da alaka da irin nauye-nauye da ke kansu kama daga kula da gida da yara baya ga aikin ko kuma sana'ar da suke yi. A cikin shekarun da suka gabata, kason mata a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag daya daga cikin uku ne kawai. Domin samun wakilci mai fa'ida da bambancin gogewa da ra'ayoyin mata, ana bukatar  adadin mata daga sassa dabam-dabam a majalisar dokokin in ji Elisa Deiss-Helbig da ta kasance jami'ar bincike a Jami'ar Konstanz da ke mai da hankali kan siyasar jam'iyyu.

Karin Bayani: Jamus: CDU ta cimma matsaya

Mata ka iya sauya manufar siyasa, wadda ba za ayi la'akari da ita ba a majalisar da maza ne mafi yawan wakilanta. Wannan yana da muhimmanci, musamman idan aka zo batun hakkin mata. A shekarar 1957 yayin da kasa da ake da kaso 10 daga cikin 100 na 'yan majalisa mata, Jamus ta kada kuri'a kan ko ya kamata magidanta su ci gaba da kasancewa masu yanke hukunci na karshe a cikin dukkan lamuran iyali?. Kuri'un mata ne suka kawo karshen wannan doka ta nuna wariya. Yawancin 'yan majalisar maza sun so ci gaba da aiki da dokar, amma kaso 74 cikin 100 na mata suka kada kuri'ar soke ta. Haka lamarin ya kasance har ya zuwa yau a Jamus, wasu canje-canje dai na bukatar kaso mafi girma na mata.