1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Tirka-tirka kafin zaben 2023

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 2, 2022

A daidai lokacin da babban zabe na shekra ta 2023 da ke tafe ke kara tunkarowa a Najeriya, ana ci gaba da samun matsaloli da rikicin cikin gida musamman a manyan jam'iyyun siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/4CDdT
Zanen Barkwanci | Siyasar Najeriya
Wa zai zabi 'yan takara a Najeriya, wakilai "deligate" ko talakawa?

Tuni dai al'amura suka yi nisa a batun zaben fitar da gwani da zai bayar da damar samar da wadanda za su tsya takara a matakai dabam-dabam, yayin babban zaben Najeriya da ke tafe a shekara ta 2023. Sai dai kuma rikicin cikin gida da zargin son kai da ma amfani da kudi, musamman a manyan jam'iyyu biyu na kasar wato APC mai mulki da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP na neman ya hana ruwa gudu.

'Ya'yan wadanna jam'iyyu dai musamman wadanda suka nuna sha'awarsu ta neman shiga a dama da sua a matakai dabam-dabam na siyasa a Najeriyar, na kokawa kan yadda kodai uwar jam'iyya ta nuna karfa-karfa wajen fitar da dan takarar da a ganinta take ganin shi zai iya lashe zaben ko kuma yadda aka yi amfani da kudi wajen sayen wakilai wato "deligate" da ke zabar 'yan takarar a yayin zabukan fitrar da gwani. 

Wadannan matsaloli dai sun janyo sauyin sheka daga wasu 'yan takarar da magoya bayansu, yayin da wasu kuma suka ci gaba da zama cikin jam'iyyun nasu amma kuma har kawo yanzu suna guna-guni. Da ma dai tirka-tirka wajen fitar da 'yan takara ba wani sabon abu ba ne a siyasar Najeriyar, musamman ma batun yin amfani da kudi ko kuma karfa-karfar masu fada a ji a jam'iyyar.