1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burundi na ci gaba da daukar dumi

Abdourahamane Hassane/ LMJJune 10, 2015

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kasar Burundi na daf da fadawa cikin wani mummunan hali na kisan kiyashi sakamakon rikicin siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/1Fek2
Pierre Nkurunziza na Burundi
Pierre Nkurunziza na BurundiHoto: Getty Images/AFP/F.Guillot

Wannan hasashe dai ya biyo bayan yadda mayakan sa kai na matasan da ke goyon bayan shugaban kasar Pierre Nkurunziza suke aikata ta'asa ga jama'a galibi fararen hula. A cikin wata sanarwa da babban kwamishinan Majalisar Dinkin Duniyar da ke kula da kare hakkin dan Adam, Zeid Ra'ad Al Hussein ya fitar a Geneva ya yi kira ga shugabannin Burundin da su gaggauta kawo karshen ayyukan kungiyar matasan ta Imbonerakure, wanda ya ce 'ya'yan ta na azabtarwa tare da kashe fararen hula.

Yiwuwar komawa gidan jiya

Mai magana da yawun babban kwamishinan Majalisar Dinkin Duniyar da ke lura da kare hakkin dan Adam, Cecil Pouily ta ce dama Burundi ta yi fama da yakin basasa na tsahon shekaru wanda a cikinsa miliyoyin mutane suka rasa rayukansu. Ta kara da cewa:

Zanga-zangar adawa da tazarce a Burundi
Zanga-zangar adawa da tazarce a BurundiHoto: Reuters/G. Tomasevic

"Maimakon a mayar da hankali wajen sake gina kasar, abin da muka lura da shi a yanzu shine kasar tana shirin komawa cikin wani hali na yakin wanda wasu tsirarun jama'a suka dage ga sake tayar da fittin."

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce, ta kan samun kira na waya kusan 40 zuwa 50 a kowace rana na mutanen da ke nema agaji da wadanda kuma ke ba da shaida dangane da abubuwan da suka fuskanta, kana kuma matasa na kungiyar ta Imbonerakure na shan arangama da jami'an tsaro.

Sacewa da barazanar kisa ga mutane

Ta'asar da kungiyoyin suke tafkawa a kan fararen hula a birnin Bujumbura da sauran garuruwa na kasar ta hada da sacewa da azabtarwa da kisa da kuma barazana. Cecila ta ce suna da wakilai a Burundin wadanda suke amsa kiran wayoyin tarho na mutane daga birane da sauran kauyukan kasar.

Wasu daga cikin shaidun da suka tsira da rayukansu zuwa Jamhuriyar Demokaradiyar kwango sun ce matasan masu goyon bayan shugaban kasar na Burundi na bi kofofin gida- gida su yi rubutun barazanar kisa. Wannan al'amari dai na faruwa ne a dai-dai lokacin da 'yan adawar kasar ke ci gaba da tayar da kayar baya ga gwamntin da ke shirin yin zabubbukan 'yan majalisun dokoki da na shugaban kasa a cikin watan Yuli mai zuwa a wani mataki na yin tazarce da shugaba Nkurunziza ke fatan yi duk kuwa da cewar doka ba ta ba shi damar tsayawa takara karo na uku a zaben shugaban kasar ba.

Al'ummar Burundi na tserewa zuwa kasashe makwabta
Al'ummar Burundi na tserewa zuwa kasashe makwabtaHoto: Getty Images/AFP/D. Hayduk