1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudani ga babban zaben Najeriya na 2015

August 4, 2014

Ya bayyana cewa kakakin majalisar wakilan Najeriya zai nemi shugabancin kasar, amma ba a jam'iyyarsa ta PDP ba. Wannan ya janyo cece-kuce kan makomar zaben kasar.

https://p.dw.com/p/1Cof0
Wahl Nigeria Proteste
Hoto: DW/U.Abubakar Idris

Bayan an kwashe tsawon lokaci ana hasashen inda ya dosa da manufar siyasarsa a Najeriya, bayyanar hotunan shugaban majalisar wakilan Najeriyar Hon Aminu Tambuwal inda aka nuna yana neman takarar shugabancin kasar a karkashin jamiyyar adawa ta APC sun jefa zahirin lamarin da ma sarkakiyar da ka iya kasancewa da ita.

To an dai dade ana zarginsa da jibintar ala'amarin jamiyyar adawa ta APC saboda haba-habar da ake ganin yana yi da ma yadda yake jan akalar shugabancin majalisar wakilan kasar, musamman sanin yadda ya kaiga darewa kan wannan mukami da a zahiri jamiyyar ta PDP bata boye rashin jin dadainta a gare shi ba.

Fitowar hotuna ya janyo cece-kuce

Bayyanar hotunan Hon Aminu Tambuwal inda aka nuna shi ya na neman takarar shugabancin Najeriyar a karkashin jamiyyar APC na zama matakin farko na kawo karshen wasan boyon da ake ganin ya dade yana yi a fagen siyasar Najeriyar. To sai dai ga Malam Buhari Jega masani a fagen siyasar kasar yana kalon lamarin ne ta fuskoki mabambamta.

Kallon da ake yi wa shugaban majalisar wakilan Najeriyar a fagen siyasar kasar musamman yadda yakan ja daga a kan al'amura da kan sa ana hangen su a rana da jamiyyarsa ta PDP ya sanya zura idanu a kan fitar da hotunan takarar na shi a wannan lokaci.

Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Ko da yake jami'in yada labaru na shugaban majalisar Imam Imam ya nisanta kansu da masaniya a kan wannan batu, amma ko wannan na nufin Hon Tambuwar na da nufin tsayawa takara a jamiyyar ta PDP ne? Ga Malam Imam Imam

Tambuwal ya shiga jam'iyyar APC a hukumance?

Ko da yake jamiyyar adawa ta APC ta ce ya zuwa yanzu dai ta san shugaban majalisar bai kai ga shigowa cikin jamiyyar ba a hukumance, amma buga takardar takara a karakashinta na da abinda yake nunawa a matsayinta a fagen siyasar Najeriyar.

A yayainda manyan jamiyyyun Najeriyar ke ci gaba da yin cirko-cirko a kan wannene za su tsayar a matsayin dan takararsu a zaben na 2015, da alamun ana ci gaba da tafka lissafi daga jamiyyun har zuwa masu sha'awar neman takara da zasu kara bayyana alkiblar irin siyasar da za'a fafata a 2015 a Najeriyar.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Pinado Abdu Waba