1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani tsakanin kungiyoyin matasa a Nijar

August 7, 2014

Takaddama ce ta kunno kai tsakanin wasu kungiyoyin matasa na kasar masu zaman kansu da kuma babbar kungiyar matasa ta kasa ta Conseil National de la Jeunesse.

https://p.dw.com/p/1Cr30
Niger Tende Festival in Zinder
Hoto: DW/L. Mallam Hami

Kungiyoyin matasan na zargin shugabannin kungiyar da yin rawa da bazar wasu 'yan siyasar kasar tare ma da neman yin tazarce a kan shugabancin kungiyar bayan da wa'adin shugabancin nasu da ya rigaya ya kawo karshe tun 'yan watanni da suka gabata. Sai dai shugabannin kungiyar matasan ta kasa sun ce batun ba
haka ya ke ba, kuma zargin da ake yi masu ba shi da tushe balantana makama.

A shekara ta 2006 ne dai gwamnatin kasar Nijar ta kafa wannan kungiya ta matasan kasar ta Nijar wato Conseil National de la Jeunesse, kamar yanda kundin tsarin mulkin kasar ya umarta. Kuma ta kunshi wakillan matasa 35 'yan shekaru 18 zuwa 32 wadanda su ka fito daga jihohi takwas na kasar, wadanda aka dorawa nauyin gudanar da fafutkar kare hakkin matasan kasar ta Nijar a tsawon wa'adi na shekaru uku kafin a gudanar da zaben maye gurbinsu da wasu sabbi.

Yanzu haka dai yau sama da watanni biyu kenan da wa'adin shugabancin kwamitin gudanarwar kungiyar ya kawo
karshe ba tare da an gudanar da zaben maye gurbin masu shugabancin na yanzu ba. Abun da kuma ya soma haifar da tashin jijiyoyin wuya daga bangaren wasu kungiyoyin matasan da ke zargin mambobin kungiyar ta kasa da gama baki da gwamnati domin yin tazarce.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar