1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon yunkurin warware rikicin Afirka ta Tsakiya

January 23, 2014

Bayan amincewa da Catherine Samba-Panza a matsayin shugabar rikon kwaryar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, ta dukufa wajen lalubo hanyar warware rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/1Aw3T
Zentralafrikanische Republik Interimspräsidentin Catherine Samba-Panza 23.01.2014
Hoto: Reuters

Masu ruwa da tsaki a sha'anin tafiyar da harkokin mulki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun zabi Catherine Samba-Panza a matsayin shugabar rikon kwarya, inda ta bukaci samun goyon bayan 'yan kasar da kuma al'ummomin kasa da kasa wajen shawo kan rigingimun dake addabar kasar, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, yayin da wasu kuma suka tsere daga matsugunansu.

Ko da shike mutane da dama sun yi fatan murabus din da tsohon shugaban wucin gadin kasar Michel Djotodia zai taimaka wajen kwantar da wutar rikicin, amma kuma har yanzu Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyan na fama da rgngimun dake da nasaba da addini da kuma kabilanci.