1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Sabuwar jam'iyyar siyasa

September 22, 2021

A yayin da ake ci gaba da neman mafitar rikici na siyasar Tarayyar Najeriya, wasu manyan 'yan boko da jiga-jigan siyasa a kasar sun kafa wata sabuwar kungiyar siyasar da suke fatan na iya kwace goruba a hannun kuturu.

https://p.dw.com/p/40fmC
Nigeria Wahlkommision verschiebt Wahltermin Attahiru Jega
tsohon shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC, Attahiru JegaHoto: Stringer/AFP/Getty Images

Kama daga ita kanta jam'iyyar APC da ta share shekaru takwasa kan mulki ya zuwa  PDP  da ta ninka dai, a idanu na da dama cikin fage na siyasar Tarayyar Najeriyar dai ana neman sauyin da ke iya daukar kasar zuwa tudun mun tsira. Batun dai ya dauki hankalin wasu 'yan boko da ma kwarraru na siyasar kasar da ke fadin da sauran sake, kuma lokaci ya iso na kawo karshen tasirin jam'iyyun guda biyu.

Karin Bayani: Mece ce makomar jam'iyyun adawa a Najeriya?

Karkashin kungiyar da suka kira ta ceton al'umma dai, jiga-jigai irin tsohon shugaban Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Najeriyar INEC Farfesa Attahiru Jega da tsohon gwamnan Kwara Abdulfatah Ahmed game da takwaransa na Cross River Donald Duke dai, sun ce tura ta kai bango kuma an kare hakurinsu. Rescue Nigeria Project dai na da burin kwace goruba a hannun kuturu a cikin siyasa ta kasar da ke dada nuna alamun babakeren manyan  jam'iyyun kasar guda biyu. To sai dai kuma tuni yunkurin nasu ya fara daukar hankali tsakanin masu siyasar Najeriya da ra'ayinsu ke rabe a kan hanyar neman mafitar.

Karikatur von Abdulkareem Baba Aminu - Nigeria APC Krise
Hoto: DW/Abdulkareem Baba Aminu

Buba Galadima dai, na zaman jagora a adawa ta kasar da kuma ya ce ana bukatar taro kafin iya kai wa ga kada guguwa ta dawa. A baya dai sai da ta kai ga hadin karfin jam'iyyu, kafin iya kai wa ya zuwa karshen mulkin PDP da ke fadin sai ta kai 60. Kuma daga dukkan alamu an yi nisa, a cikin tattaunawa da kokarin hadin gemu da nufin iya kai wa ga cimma bukatar da ke iya bude sabon babi ga makomar fagen siyasar Najeriyar. Shehu Musa Gabam dai na zaman sakataren jam'iyyar SDP na kasa, daya kuma cikin jam'iyyun da ke fadin sun nisa a kokari na kulla kawancen kai manyan jam'iyyun zuwa gidan tarihi.

Karin Bayani: Barazanar 'yan siyasa ga tasirin kotuna a Najeriya 

Koma wane irin tasiri gangamin korar masu tsintsiyar ke iya yi a kokari na sauya rayuwar al'ummar Najeriyar dai, daga dukkan alamu akwai jan aiki a tsakanin masu tunanin kwatar mulkin daga hannun wadanda giyar mulkin ke kara bugarwa cikin kasar a halin  yanzu. Kuma ma a fadar Faruk BB Faruk da ke sharhi a siyasa ta kasar, babu lokacin iya samun nasara ta hadakar cikin kasar da ke da kasa da wattani 18 zuwa babban zabe na gaba. Jan aikin da ke gaban 'yan sauyin dai na zaman bambance akidar da kokari na neman damar taka rawa a cikin tsarin da ke dada nuna alamun mai karfi sai Allah.