1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Buhari alkawuran baya ba gamsarwa

Adrian Kriesch
February 15, 2019

Shugaba Buhari na neman wa'adi na biyu a babban zaben da zai gudana ranar Asabar a Najeriya. Shekaru hudu baya ya yi alkawura da dama, to amma kusan babu gamsarwa a cewar wakilin DW a Najeriya Adrian Kriesch.

https://p.dw.com/p/3DTyD
Nigeria Wahlkampf
Hoto: Reuters/A. Sotunde

A farkon shekara ta 2015 dubun dubatar 'yan Najeriya ne suka yi dandazo kan titi a birnin Kano rike da fastoci na hotunan Muhammadu Buhari da kuma tsintsiya da ke zama alamar jam'iyyarsa ana ta doki. Buhari ya yi wa magoya bayansa da suka hallara a filin yakin neman zaben alkawarin yaki da cin hanci da ya yi katutu a kasar. Buhari dan siyasa ne da masu adawa da shi ma suka yarda cewa adali ne. A zaben 2015 wani bangare na al'ummar Najeriya sun yi wa Buharin kallon wani mai ceto. Amma ba a samu yadda ake so ba domin uku daga cikin alkawuransa na zabe ba su samar da sakamako na a zo a gani ba.

Buhari ya yi alkawarin magance matsalar tsaro, ko da yake a farkon kama madafun iko an samu ci-gaba a yaki da 'yan Boko Haram a Arewa maso Gabas amma a lokaci guda wasu rigingimu sun kunno kai, kamar rikicin manoma da makiyaya a yankin Arewa maso Tsakiya da matsalar garkuwa da mutane a Kaduna da 'yan bindiga a Zamfara. Buhari ba ya saurin daukar mataki har sai abun ya kusan baci. A Niger Delta an samu kwanciyar hankali domin gwamnatin Buhari ta ci gaba da biyan tsoffin 'yan bindiga na yankin.

Nigeria Flüchtlingscamp in Maiduguri
Miliyoyin 'yan Najeriya sun zama 'yan hijira a cikin kasarsuHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Sai dai halin da ake ciki a Arewa maso Gabas ya sake rincabewa inda cikin watanni uku da suka wuce mutane kimanin dubu 60 suka tsere daga yankunansu, yayin da garin Rann da aka taba kai wa farmaki ta sama bisa kuskure, Boko Haram ta sake kai hari, lamarin daya tilasta dubbai tserewa zuwa kasar Kamaru. Me ya sa hakan ke sake faruwa? Me ya sa sojoji suka kasa shawo kan lamarin duk da miliyoyi dubbai na kudade da ake ware musu daga kasafin kudin kasa? Maimakon samar da zaman lafiya a 2018 sojoji sun sake bude wuta kan 'yan Shi'a a kusa da Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Kamar yadda aka saba a gwamnatin Buhari, ba a dauki wani mataki ba in ban da bincike da sojojin kansu suka ce za su yi, binciken kuma da babu wani sakamako na hakika.

Alkwarinsa na biyu shi ne yaki da matsalar rashin aikin yi, amma tun bayan hawan mulkinsa yawan marasa aiki ya tashi daga kashi 8.2 zuwa kashi 23.1 cikin 100. Ko da yake babu mai yaba masa amma kuma babu mai zarginsa, domin Buharin ya kama ragamar mulki lokacin da baitul-malin kasa ke wayam kuma farashin man fetur da kasar ta dogara da shi ya fadi kasa warwas. Manufarsa dangane da fadada fannonin tattalin arziki da farfado da masana'antu na cikin gida ke da muhimmanci. Sai dai a nan ma kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Nigeria Präsidentschaftswahl 2015 Atiku Abubakar
Wannan dai na zama dama mai karfi ga AtikuHoto: DW/U. Musa

Yana ci gaba da yaki da cin hanci da ke zama alkwarinsa na uku. Amma a kasa irin Najeriya da cin hanci ya zama ruwan dare, ba abin mamaki ba ne da yaki da matsalar ke tafiyar hawainiya.

Hakika hakan na nufin faduwar Buhari a zabe, amma saboda da dalilai guda biyu ba za a kai ga wannan ba. Na farko shugaban na da miliyoyin magoya baya a arewa. Na biyu babu wani zabi ma fi kyau ga 'yan Najeriya da dama kamarsa. Babbar jam'iyyar adawa ta PDP da ta yi mulki tsawon shekaru 16 ba ta ciyar da kasar gaba ba. Dan takararta Atiku Abubakar da ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasa tsawon shekaru takwas bai gabatar wa masu zabe wata kwakkwarar manufa dangane da makomarsu ba. Duk da haka dai za a yi kankankan a zaben tsakanin Buhari da Atiku.