Shekaru 10 da fara rikicin Boko Haram a Najeriya
August 1, 2019Talla
Yayin da aka ciki shekaru 10 da fara rikicin Boko Haram bayan kashe shugabanta na farko Muhammad Yusuf da jami'an tsaro suka yi lokacin yana hannunsu, har yanzu an kasa kawo karshen rikicin. Ana iya cewa kashe jagoranta ya haifar da rikicin na Boko Haram da aka kwashe shekaru 10 ana fama da shi wanda ya bazu zuwa wasu jihohin Najeriya da ma kasashen makwabta kamar Chadi da Kamaru gami da Jamhuriyar Nijar.