A cikin shirin za a ji cewar hukumar shige da fice ta Najeriya ta ce ba gudu ba ja da baya a ci gaba da rufe kan iyakokin kasar ta. A jamhuriyar Nijar kuwa kasar ke cikin kasashen da ke fama da azabar yunwa, a cewar wani sabon rahoton kungiyar yaki da yunwa ta duniya.