1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikita-rikitar siyasa a Jamhuriyar Nijar

Salissou BoukariOctober 15, 2015

Batun kirkiro da sababbin jam'iyyun siyasa a Jamhuriyar Nijar, da ma rashin mutunta demokaradiyya a cikin jam'iyyu na ci gaba da janyo cece-kuce.

https://p.dw.com/p/1GoqV
Mahamadou Issoufou
Mahamadou IssoufouHoto: F. Batiche/AFP/Getty Images

A yayin da zabuka a Jamhuriyar Nijar ke kara gabatowa, ana ci gaba da samun rikicin siyasa, yayin a hannu daya batun kirkiro da sababbin jam'iyyun siyasa barkatai ke ci gaba da shan suka daga 'yan kasar, a daya hannun kuma ana zargin wasu jam'iyyun siyasar kasar har ma jam'iyya mai mulki da rashin mutunta ka'idojin demokaradiyyar.