1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojan Nijar sun yi fata-fata da 'yan Boko Haram

Salissou Boukari YB
January 3, 2019

A kokarin yakar 'yan ta'adda musamman ma mayakan Boko Haram a gabashin kasar Nijar iyaka da Najeriya, sojojin Nijar da suka kaddamar da wani farmaki sun yi nasara kan mayakan na Boko Haram tare da kwace kayayyakinsu.

https://p.dw.com/p/3AyvQ
Soldaten im Niger
Hoto: Desmazes/AFP/Getty Images

A Jamhuriyar Nijar sojojin gwamnatin kasar sun yi nasarar halaka mayakan Boko Haram kimanin 300 a wani farmaki ta kasa da ta sama da suka kaddamar kansu a yankin tabkin Chadi. Tun daga ranar 28 ga watan Disamba ne dakarun suka fara ruwan makamai kan mayakan.

A cikin wata sanarwa da  ta fitar a ranar Laraba wadda sashen Hausa na DW ya samu kwafinta, ma'aikatar tsaron kasar Nijar ta ce baya ga mayakan na Boko Haram sama da 200 da jiragen yakin sama na kasar suka kashe, suma sojojin da ke kasa sun yi nasarar halaka mayakan na Boko Haram 87 kana suka lalata kwale-kwale guda takwas da suke amfani da su.

Soldaten im Niger
Hoto: Desmazes/AFP/Getty Images

Kazalika sun karbo motoci uku da manyan bindigogi da suka hada da masu aman harsasai guda biyu da na harba rakoki guda biyu da kuma harsasai sama da 2000 da wayoyin salula takwas da kuma tarin miyagun kwayoyi. 

Da dama dai al'ummar kasar ta Nijar hadi da 'yan fafutika sun nuna farinciki da yadda mayakan ke shan lugudan soja, sai dai sun kara kira su kara zage damtse haka gwamnati ta ba su gudunmawar da ta dace.

Ma'aikatar tsaron kasar ta Nijar ta ce babu asara rai ko ta dukiya da aka samu daga bangaran sojojin na Nijar a cikin wannan farmaki wanda suka kaddamar tun a ranar 28 ga watan Disamban da ya gabata a yankin gabar kogin Komadougou na kan iyaka da Najeriya da kuma a kananan tsibirrai da ke a yankin Tafkin Chadi da ke zama mabuyar mayakan na Boko Haram.