1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tsaro kan Boko Haram a Nijar

Yusuf BalaOctober 7, 2014

Dukkanin shugabannin kasashe da ke makwabtaka da Najeriya sun tattaru a Nijar a wajen taron banda shugaban kasar Kamaru

https://p.dw.com/p/1DRnF
Verteidigungsminister der Mitgliedsstaaten von CBLT
Hoto: DW/M. Kanta

Mahukunta daga Najeriya da makwabtanta sun tattaru a kasar Nijar me makwabtaka da Najeriyar a ranar Talatannan, dan tattaunawa kan hanyoyi na bai daya da za a bi wajen ganin bayan Kungiyar Boko Haram.

Shugabannin da suka hadar da Goodluck Jonathan na Najeriyar da Mahamadou Issoufou na jamhuriyar Nijar da Idriss Deby na Chadi da Thomas Boni Yayi na Jamhuriyar Bene sun tattaru a birnin na Niamey fadar gwamnatin kasar ta Nijar dan tattauna yadda za a samar da ayyukan soja na hadin gwiwa dan fatattakar mayakan na Boko Haram.

Kasar Kamaru me makwabtaka da Najeriyar dai daga kudu maso gabashi wacce ita ma ta sha fama da ayyukan kutse na masu tada kayar bayan daga Kungiyar ta Boko Haram, ministan harkokin wajenta shi ne ya wakilceta a wurin taron.

A watan Yuli dai Niger da Najeriya da Chadi da Kamaru, kowannensu ya yi alkawarin bada sojoji 700 dan samar da tawagar sojan hadin gwiwa na kasa da kasa da za su yi aiki kafada da kafada wajen yaki da kungiyar Boko Haram wacce ke da tushe daga Najeriya da tuni ta hallaka sama da mutane 10,000 tun daga shekarar 2009.

A cewar mai masaukin baki Muhammad Issoufou shugaban kasar ta Nijar, yaki da wannan mayaka na Boko Haram na bukatar hakikanin hadin kan kasashe baki dayansu ta yadda zasu yi aiki tare su kai ga nasara.