1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dambarwar siyasa a Nijar

December 30, 2013

Wani sabon takon saka ya kunno kai tsakanin jam'iyyun adawa da gwamnatin jamhuriyar Nijar bayan manyan tarukan da bangarorin biyu suka yi a karshen mako.

https://p.dw.com/p/1AijE
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: Seyllou/AFP/Getty Images

Shugabannin jam'iyyun adawar kasar suna fargabar barzanar daukar matakin rushe jam'iyyun siyasa. 'Yan adawar sun yi wannan zargi ne biyo bayan babban taron Congres na kasa na jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki a birnin Yamai inda aka zabi Mallam Muhammed Bazoum shugaban riko na jam'iyyar a matsayin sabon shugaban mai cikakken iko, a wani sabon wa'adi na shekaru hudu masu zuwa.

Sai dai a jawabinsa na rufe taron Mallam Muhammed Bazoum ya kalubalnci 'yan adawa da zargi kan hujjar Muhammadou Issofou cewa ta kasa tafiyar da mulki da kuma neman wargaza tafarkin demokradiyya yana mai:

Außenminister der Republik Niger
Muhammed BazoumHoto: DW/T.Mösch

"Na sha alwashi kuma ina mai jaddada cewar cikin kwanaki kalilan za su gani."

Kokarin yi wa doka karar tsaye

Wadannan kalaman sun sosa zukatan 'yan adawa wadanda suka mayar da martani cikin kakkausar murya. Mohammed Murtala wani jigo ne a jam'iyyar MNSD Nasara wadda ke cikin kawancen jam'iyyun adawa:

"Ko da ya ke dukka matakin da suka dauka na boye da na filin, mun ga na filin, kuma na boyen mun san suna da tsarin soke jam'iyyu da yawa kamar wadanda ba su kan ka'ida wadanda ba su yi Congress ba a kan lokaci. Muna jiran wannan lokacin, saboda Nijar kasa ce wadda ta takli demokradiyya kuma akwai dokoki. Saboda haka babu wani mahalukin da zai fito ya ce ya dakatar da jam'iyyu ba bisa kan gaskiya ba."

Oppositionspartei im Niger
Alhaji Saini Oumarou na jam'iyyar MNSD NasaraHoto: DW/M. Kanta

Mohammed Murtala ya kara da cewa "za su yi fito na fito da duk wanda ya ce zai yi kama karya a cikin kasar ta Nijar."

Sabon shugaban jam'iyyar PNDS Tarayya ya yi magana game da zargin 'yan adawa da ake yi na sata dukiyar kasa da cin hancin da kuma ta'asar da suka tabka.

Sai dai 'yan adawar sun yi mayar da martani da cewa doka dai daga gida take farawa, kuma matukan mutum yana son ya gwada kyakkyawan misali to ya fara da gidansa.

Wannan zazzafan rikicin siyasa da ya kunno a Jamhuriyar ta Nijar ba farau ba Nijar din ta saba samun kanta a cikin wannan dambarwar siyasa wadda ma ke ba da kafar mai da hannun agogo baya a kokarin shimfida kyakkyawan tafarkin demokradiyya.

Mawallafi: Mahaman Kanta
Edita: Mohammad Nasiru Awal