1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya da EU na duba makomar 'yan gudun hijira

Umaru Aliyu/YBOctober 5, 2015

Shugaban Turkiya, Recep Tayyip Erdogan na Bruessels, inda yake ganawa da shugabannin kungiyar hadin kan Turai, kan hanyoyin hadin kai tsakaninsu game da matsalar kwararar 'yan gudun hijira zuwa nahiyar.

https://p.dw.com/p/1Gj0u
Brüssel Jean-Claude Juncker Treffen mit türkischem Präsidenten Tayyip Erdogan
Shugaba Tayyip Erdogan da Jean-Claude Juncker a birnin BrüsselsHoto: Reuters/F. Lenoir

Cikin wadanda Erdogan yake ganawa da su, har da shugaban kungiyar ta hadin kan Turai Donald Tusk da shugaban hukumar kungiyar, Jean Clade-Juncker da kuma shugaban majalisar dokokin Turai, Martin Schulz.

Kungiyar Hadinkan Turai ana sa ran za ta nemi taimako da hadin kan kasar Turkiya, game da dakatar da kwararowar dimbin 'yan gudun hijira daga yankin Gulf da Gabas ta Tsakiya zuwa nahiyar Turai, musamman zuwa kasashen kungiyar ta EU. Tun kafin ya isa Brussels, sai da kakakin kungiyar hadin kan Turai, Margaritis Schinas ya ce burin ziyarar ita ce shigar da Turkiya cikin duk wani mataki na kawo karshen kwararar 'yan gudun hijira zuwa wannan nahiya, musamman ganin cewar da yawa daga cikin 'yan gudun hijirar sukan yi amfani da Turkiya a matsayin wurin yada zango, kafin su karaso zuwa Turai.

Nahiyar dai tana fama da matsalar 'yan gudun hijira da ke kwararorowa musamman daga Siriya, abin da masana suka ce matsalar ita ce mafi muni tun bayan kare yakin duniya na biyu. Ita kanta Turkiya ta karbi 'yan gudun hijira kimanin miliyan biyu a cikinta, yayin da mafi yawansu suke fatan samun damar tsallakawa zuwa kasashen kungiyar hadin kan Turai, musamman Jamus.

Belgien Präsident Recep Tayyip Erdogan in Brüssel
Masu tarbar shugaba Erdogan a BrüsselsHoto: F. Florin/AFP/Getty Images

Wannan matsala ma ita ce yanzu haka ta mamaye al'amuran siyasa a kasar ta Jamus, inda jam'iyyu suke ci gaba da zargin junansu da goyon baya ko adawa da ci gaba da kwararowar masu neman mafakar siyasa zuwa cikin kasar. A wannan shekara ana sa ran 'yan gudun hijira kimanin miliyan daya da rabi ne za su shiga Jamus domin neman mafakar siyasa. To sai dai ma'aikatar cikin gida ta musanta wannan kiyasi, tare da nunar da cewar babu wanda ya san yawan bakin haure da kasar za ta karba ya zuwa karshen shekarar. Kakakin ma'aikatar, Harald Neymanns ya ce:

"Da farko dai ba zan iya tabbatar da alkaluman da akai ta yadawa tun daga jiya ba. Abin da kadai zan iya tabatarwa kamar yadda na sha yi a can baya, kuma shima minista ya sha fada shine, yawan yan gudun hijiran da suka shigo kasarmu yanzu haka suna da yawa. Muna kuma zaton cewar watan Satumba da ya gabata zai zama watan da ya fi samun kwararar 'yan gudun hijira cikinsa zuwa Jamus tsawon shekaru da dama".

A tattaunawar da zai yi da shugabannin kungiyar hadinkan Turai lokacin ziyarar tasa a Brussels, ana sa ran zai duba yadda za a karfafa hadin kai game da rage kwararowar 'yan gudun hijiran zuwa Turai, inda aka ce ya zuwa daya ga watan Oktoba, 'yan gudun hijira akalla dubu 390 ne suka bi ta kasar ta Turkiya zuwa Girka. Kungiyar hadinkan Turai ta yi wa Turkiya alkawarin kudi misalin Euro miliyan dubu daya idan har ta hada kai aka dakatar da kwararar 'yan gudun hijirar.

A birnin Berlin, kakakin jam'iyar Greens a majalisar dokoki ta Bundestag, Anton Hofreiter yayi gargadi a game da abin da ya kira, cimma yarjejeniya ta haramun tsakanin kungiyar hadinkan Turai da Turkiya, wadda a karkashinta, za a kyale Turkiya ta karbi mafi yawan 'yan gudun hijira, yayin da sauran kasashen Turai za su rufe idanunsu ga batun kare hakkin 'yan Adam da bukatar 'yan gudun hijira ta samun taimako.

Türkei Griechenland Flüchtlinge bei Edirne
'Yan gudun hijira a iyakar TurkiyaHoto: Reuters/O. Orsal

Tun da yammacin Litinin din nan, shugaban na Turkiya, Erdogan ya gana da Donald Tusk, shugaban majalisar Kungiyar hadinkan Turai. Bayan batun 'yan gudun hijira, sauran al'amuran da suka duba sun hada har da yadda za a karfafa kusantar juna tsakanin kasar ta Turkiya da Kungiyar EU da kokarin da kasar take yi na kasancewa wakiliya a wannan kungiya. Tun da bangarorin biyu suka fara tattaunawa kan haka tsakaninsu a shekara ta 1987, babu wani ci gaba na azo a gani da aka samu.