1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargaba kan kisan kananan yara a yankin Sahel

Gazali Abdou Tasawa MNA
January 28, 2020

Asusun Unicef ya bayyana damuwa kan kashe-kashen kananan yara a tashe-tashen hankulan da ke faruwa a kasashen tsakiyar yankin Sahel musamman a kasar Mali.

https://p.dw.com/p/3WtwF
Mali Gao Operation Barkhane Kinder und französische Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/P. Desmazes

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya wato Unicef ya bayyana damuwa kan yadda aka fuskantar kashe-kashen yara kanana da raba su da iyayensu a tashe-tashen hankullan da ke wakana a kasashen tsakiyar yankin Sahel na Mali, Burkina Faso da Nijar.

A wani rahoto da ya fitar a wannan Talata asusun na Unicef ya ce a kasar Mali kadai an halaka kananan yara 277 ko kuma nakasa su a watanni tara na farkon shekara ta 2019, adadin da ya nunka gida biyu na shekara ta 2018.

Asusun na Unicef ya ce ko da shike cewa a halin yanzu alkalumman kasar Malin ne kawai yake da a hakumance kan wannan mummunan yanayi da yaran ke ciki, a kasashen Burkina Faso da Nijar ma akwai darururuwan kananan yaran da suka tsinci kansu a cikin irin wannan matsala, inda ko baya ga kashe su, mayakan kungiyoyin 'yan ta'adda ke sace su, suna yi masu fyade ko kuma tilasta masu shiga yaki.