1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ta kara wa'adin sojojinta a Afirka

Yusuf Bala Nayaya
April 3, 2019

Kimanin dakarun sojan Jamus 900 ya zuwa yanzu an jibge su cikin rundinar MINUSMA a Mali da Nijar domin tallafa wa aikin dakile 'yan tawaye masu da'awar Islama.

https://p.dw.com/p/3GAiP
Mali Gao Bundeswehr MINUSMA
Hoto: Getty Images/A. Koerner

Majalisar ministocin Jamus ta kara wa'adin aiyuka uku na sojan Jamus da ke wakana a Afirka. A cewar majalisar ministocin aikin ba da horon sojoji na EUTM a Mali da MINUSMA da aikin maido da zaman lafiya na MDD a Mali za su ci gaba da wakana ba tare da fuskantar tangarda ba.

Kimanin dakarun sojan Jamus 900 ya zuwa yanzu an jibge su cikin rundinar ta MINUSMA a Mali da Nijar domin tallafa wa a dakile aikin 'yan tawaye masu da'awar Islama, kimanin dakarun 1,100 ne dai ake son kaiwa.

Dakarun da ke ba da horon daga Turai na EUTM a Mali na samun jagoranci na Jamus tun daga watan Nuwambar 2018. Yanzu akwai dakaru 180 da ke aikin da ake son tura dakaru 350. Yanzu dai wannan matsaya da majalisar ministocin ta tsayar za ta jira ji daga bangaren majalisar dokokin Jamus matakin da ke zama cikon sharuda ne kawai.