1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijirar Najeriya na Fama da matsaloli.

Salissou BoukariMarch 10, 2015

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya CICR, ta nuna damuwarta kan halin da dumbun 'yan gudun hijirar Najeriya da ke yankunan tafkin Chadi ke ciki a halin yanzu.

https://p.dw.com/p/1EoAa
Hoto: S. Girard

Matsalar Boko haram da ake fama da ita yanzu haka a Tarayyar ta Najeriya, ta tilastawa dubunnan mutane barin matsugunnansu ya zuwa kasashen makwabta na Kamarun, Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar, inda kawo yanzu halin da 'yan gudun hijirar ke ciki ke kara tabarbarewa a cewar wannan Kwamiti.

Yayin wani taron manema labarai a yau din nan a birnin Geneva, kakakin hukumar agajin ta CICR Jean-Yves Clémenzo, ya sanar cewa suna a matsayin shaidu na halin matsin da 'yan gudun hijirar na Najeriya da ke kasashe makwabta ke ciki. Rikicin na Boko Haram dai ya yi sanadiyar rasuwar mutane fiye da 13.000 tare da tilastawa wasu fiye da milian daya da 500 barin matsugunnan su daga shekarar 2009 kawo yanzu.