1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda na kokarin gano basaraken da aka sace

Abdullahi Maidawa Kurgwi AA
November 21, 2018

Rundunar 'yan sandan jihar Plateau da ke Najeriya, ta ce jami’anta suna kan kokarin gano wadanda suka yi garkuwa da wani basaraken gargajiya mai daraja ta biyu a karamar hukumar Shendam da ke jihar.

https://p.dw.com/p/38gRG
Nigeria Polizei
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Tun a ranar Talata ne dai rundunar 'yan sanda na jihar Plateau ta sanar cewar wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da wani basaraken karamar hukumar Shendam. Ko da yake akwai rahontannin da ke nuna cewa wai an sako shi daga baya, amma mataimakin Sifiritandan 'yan sanda Terna Tyopev ya sanar da cewa sun dukufa wajen nemo inda basaraken yake, a hirarsu da wakilin DW a jihar Plateau, Abdullahi Maidawa Kurgwi.

 A cewar Terna Tyopev  burinsu shi ne su gano inda basaraken yake, domin sun baza ma'aikatansu don gano inda 'yan bindigar suke buya, kuma za su sanar da jama'a halin da ake ciki da zarar sun cimma nasara.

Polizei in Nigeria
Hoto: Tony Karumba/AFP/Getty Images

Wannan lamari na sace-sace dai ya yawaita sosai inda a baya aka sace wani basarake a jihar Kaduna na masarautar Adara da ke karamar hukumar Kachia, Mr. Maidawa Galadima, lamarin da ya zamo ajalinsa. Wannan ya janyo sharhi daga masharhanta kamar su Shu'aibu Zakari Lamba, wanda da ke yin kira ga hukumomi cewa suke bayar da kariya ga sarakunan gargajiya ganin matsayinsu ga al'umma. 

To sai dai a cewar Usman Abubakar wani da ke bin labarin sace basaraken, lokaci ya yi da hukumomi za su tashi tsaye kan wannan sabon salon na garkuwa da sarakunan gargajiya.

Kawo yanzu dai, babu wani karin bayani daga jami'an tsaro kan batun gano wannan basaraken na gargajiya na kasar Dorok da ke karkashin garin Shendam a jihar Plateau.