1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya ce ya yi nasarar lashe zabe

November 4, 2020

Ga dukkan alamu an kama hanyar jefa sakamakon zaben Amirika cikin rudani, bayan da Shugaba Donald Trump ya yi wasu kalamai masu sosa zuciya da ban mamaki, da ake ganin sun sabawa turbar dimukuradiyya.

https://p.dw.com/p/3krbH
US Wahl 2020 Donald Trump
Shugaba Donald Trump ya yi ikirarin lashe zabe da barazanar tafiya kotuHoto: Chip Somodevilla/Getty Images

Kalaman na shugaban Amirkan Donald Trump dai, na zuwa ne gabanin kammala kidaya kuri'un da miliyoyin Amirkawan suka kada a ranar talatar da ta gabata yana mai cewa: "Mun kama hanyar yin nasara a wannan zabe. A fili yake cewa mun lashe zaben.

Wannan riga malam Masallaci da Trump ya yi, a daidai lokacin da ake ci gaba da kirga kuri'u a jihohin raba gardama irinsu su Michigan da Pennslyavania da Wisconsin, duba da yadda dunbin magoya bayansa suke yarda da dukkan wani zargi da yakan yi, a kasar da dama tuni sigar siyasar wannan zamani ta riga ta raba kan jama'a sosai, zai iya yin mummunan tasiri ga sakamakon zaben. Mai sharhi kan al'amuran siyasa, Abby Philip ta ce: "Ina jin cewa Dimukuradiyyarmu na cikin hadari."

Karin Bayani: Amirka: Tsarin zababbun wakilai na jihohi

Har ya zuwa lokacin da Trump ya yi ikirarin lashe zaben, bai kama kafar mai hamayya da shi ba Joe Biden na Democrats, a tseren da suke yi na samun kujeru 270 da za su ba dan takara nasara, duk da cewa Trump ya lashe jihohin Taxes da Florida da Ohio.
Sabanin irikarin lashe zabe maras tushe da Trump ya yi, shi kuwa Joe Biden ya bai wa magoya bayansa hakuri ne cewa, mai yiwuwa a dauki lokaci ana kirga kuri'u kafin a san wanda ya lashe zaben: Ba aikina ba ne ko na Donald Trump fadin wanda ya yi galaba a wannan zabe. "Wannan hukunci ne da Amirkawa za su yanke, amma ina da kwarin gwiwa game da yadda sakamakon zai kasance."

US Wahl 2020 Joe Biden
Dan takarar jam'iyyar adawa a shugabancin kasar Amirka Joe Biden Hoto: Angela Weiss/AFP/Getty Images

Karin Bayani: Zaben Amirka: Al'umma cikin zaman dar-dar

Za dai a iya cewa Shugaba Trump a fakaice na son a dakatar da kirga kuri'u a wasu jihohin, sakamkon jawabin nasa da kuma barazanar tafiya kotun koli da ya yi, a daidai wannan lokaci da masu sharhi kan al'amura irinsu Lauyan jam'iyarsa ta Republican Benjamin Geinsburg suke nuna takaicin wasu kalaman da suke fitowa daga bakin shugaban na Amirika: "Abin da shugaban ya fada ba kawai ya sabawa al'ada ba ne, bai da madogara a doka, kuma tamkar yin yankan baya ne ga dukkan maza da matan da suka kada kuri'unsu."

Bincike ya nuna cewa, yayin da jam'iyyar Republican ta ware wasu milyoyin daloli domin hidimar zuwa kotuna, ita kuma Democrats ta tanadi lauyoyi 600 da za su tsaya mata a matakai dabam-dabam na karararrakin da za a kai, game da wannan zabe na bana mai cike da riciki.