1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben jin ra'ayin jama'a a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Zainab Mohamed AbubakarDecember 11, 2015

Al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na shirin kada kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan sabon kundin tsarin mulki a wani mataki na share fagen sauran zabukan kasar masu zuwa.

https://p.dw.com/p/1HM9A
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Dibert

Wani dan kasar ta Afirka ta Tsakiya da ke shige wa a birnin Bangui, fadar gwamnati dai ya ce bashi da masaniya dangane da yadda zai kada kuri'ar. Duk da cewar ba'a wayar da kan jama'a dangane da yadda kuri'ar jin ra'ayin take ba, kowa na muradin ganin yadda abun zai kasance. Da ya wa daga cikin 'yan kasar dai ba su san komai game da sabon kundin tsarin mulki da ake muradin su jefa kuri'ar jin ra'ayin jama'a a ranar lahadi ba. Daya daga cikin dalilai da ke dasa shakku a zukatan jama'a dai shi ne yadda ake ci gaba da samun nau'o'i daban daban na kundin ta yanar gozo, batun da ke dasa aya akan shin wanne ne ainihin kundin na gaskiya. Manazarci kan lamuran siyasa daga cibiyar nazarin kasashe na Jamus da ke Hamburg Tim Glawin, ya ce bayan daukar tsawon lokaci yana nazarin nau'i daban daban na kundin tsarin mulkin, ya gaza tantance kowanne daga cikinsu za'a gabatar domin jin ra'ayin jama'a....

Zentralafrikanische Republik Menschen in der Hauptstadt Bangui UN Blauhelme
Hoto: Reuters/S. Rellandini

"Na yi imanin cewar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na fuskantar matsin lamba daga kasashen ketare. Kai tsaye zan iya cewar akwai matsin lamba daga jakadan Tarayyar Turai da na Faransa. Su na muradin ganin cewar an gudanar da zaben tare da sakamako, domin su ce yanzu aikin mu ya kare za mu iya tafiya ".

Mako guda kenan aka kaddamar da kampen na wayar da kan al'ummar kan sabon kundin tsarin mulkin. 'Yan siyasa dake gwamnatin rikon kwarya sun yi amfani da jaridu wajen yayata kundin. Manufarsu ita ce a tsara gudanar da kuri'ar sa'annan a samu amincewa daga bangaren jama'a. Modibo bachir Walidou da ke zama ministan gudanarwa a gwamnatin rikon kwaryar, ya yi kira ga al'umma da su jefa kuri'ar amincewa da sabon kundin tsarin mulkin kasar....

Zentralafrikanische Republik Marktszene in der Hauptstadt Bangui
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

" Kundin ya tanadar da cewar, ko wane yanki na kasar zai samu wakilci a cikin gwamnati. kuma wannan wani mataki ne na ci gaba".

Bai wa yankunan kasar damar taka rawa cikin harkokin gwamnati dai, ya kasance babban batu a lokacin da ake tsara kundin. Ana ganin cewar kuri'ar amincewa da kundin da za'a gudanar, da kuma zaben 'yan majalisu da na shugaban kasa a Afirka ta Tsakiyar dai, wani mataki ne na tsamo kasar daga hali na tsaka mai wuya da ta tsinci kanta na rigingimu da ke da nasaba da addini da kabilanci. A watan Maris na 2013 ne dai 'yan adawan Seleka wadanda akasarinsu muslimi ne suka kifar da gwamnatin Francois Bozize inda a matsayin martani mayakan Anti balaka wadanda akasarinsu kristoci ne da ke goyon bayan hambararren shugaban kasar suka afkawa musulmi. Tun daga wannan lokacin ne kasar ta fada rigingimu na addini, da ya haddasa asarar rayukan dubban mutanen kasar.