1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar Ɗalibai a jamhuriyar Nijar

February 18, 2013

Ɗaliban na gangamin nuna baƙin cikinsu ne ga kisan gillar da jami'an tsaro suka yi wa wani ɗalibi a yayin gudanar da binciken kwakwab a birnin Gaya.

https://p.dw.com/p/17gf4
Auf dem Bild: Studentendemo in Zinder, Niger. Bild. DW / Larwana Hami
Studentendemo Zinder NigerHoto: DW/L.Hami

Tun da sanyin safiyar litinin ɗin nan ce, Ɗalibai na jami'ar birnin Tahoua na ƙungiyar USN suka fito dafifi bisa tituna domin nuna baƙin cikin su kan kisan gillar da aka yi wa wani Ɗalibi ɗan uwan su a can birnin Gaya na jihar Dosso, sakamakon wata rigima da ta ɓarke tsakanin al'ummar garin da jami'an tsaro na 'yan sanda sakamakon matsin kaimi da jamiyan tsaro kan yi wa al'umma a fuskar binciken kwakwab na ababan hawa tare da ci musu mutunci.

Abun da ya kawo tashin hankalin da ya haddasa rasuwar ɗalibin mai suna Mamane Zayyanu Hassan sakamakon halbin sa da akayi a kai, a halbe halben kan mai uwa da wabi da jami'an tsaron suka yi.Hakan ya sanya Komitin zartarwa na ƙungiyar ɗaliban Nijar ta ƙasa baki ɗaya ta kira wannan jerin gwano na ƙasa domin nuna baƙin ciki kan abun da ya faru ga ɗalibin ɗan uwan su.
Ita dai wannan zanga zanga a nan Tahoua an yi ta ne da manufa
Paraizo Hassoumi Umaru shine mataimakin shugaban ƙungiyar ɗalibai na jami'ar birnin Tahoua ya yi tsokaci kan wannan batu

" Gaskiya abun bai mana daɗi ba domin abu ne da bai cancan ci ace ya kawo wannan lokaci ba'a shayo kanshi ba dan haka ne ma muke ganin cewa tamkar ba'a ɗauki karatu da wani mahimman ci ba a nan Tahoua, har yanzu sati guda ba'a shawo kanshi ba amma yanzu muna ganin za'a shayo kan matsalar.
Da yake magana a gaban Ɗaliban yayin da suka iso offishin gomnan jihar Tahoua Sakatare janar na Offishin gomnan jihar ta Tahoua yahaya Tankari ya yaba ma Ɗaliban dangane da yadda suka fito cikin lumana tare kuma da yin Allah wadai da abun da ya faru a can Gaya.

Auf dem Bild: Studentendemo in Zinder, Niger. Bild. DW / Larwana Hami
'Yan makaranta sun ƙona motar magajin garin Zinder yayin zanga-zangaHoto: DW/L.Hami
Gabon Studenten Proteste in Libreville Archiv 18.04.2012
Ɗalibai a GabonHoto: Tiphaine Saint-Criq/AFP/Getty Images

Arangamar da ta haddasa rasuwar wannan dalibi, mai suna Zaiyyanu Hassan Allah ya jikan sa, ta ɗauki tsawon kwanaki uku ana yinta a can birnin Gaya tsakanin al'ummar gari da jamiyan tsaro na 'yan sanda abun da ya kawo sai da Gomnan jihar Dosso tare da rakiyar Darecta Janar na Police na ƙasa baki ɗaya, inda suka halarci jana'izar wannan ɗalibi, sannan suka tattara dukkan ɓangarorin dake hamayya a zauren shawara guda domin sasanta tsakani domin magance matsalar, sannan kuma aka sanya jamiyan bincike domin gano masu laifin abubuwan da suka wakana, sai dai a cewar ɗaliban wannan bicike na jeka nayi ka ne ganin cewa a kullu yaumin da zarar irin haka ta faru a kan shirya bincike amma a cewar su basu taɓa ganin sakamakon binciken ba.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohammed Abubakar