1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar dalibai a Nijar

March 20, 2014

Kungiyoyin daliban Nijar na zargin gwamnati da rashin cika alkawuran da ta yi musu na samar da isassun wurare da kayayyakin karatu dan bunkasa illimi a kasar

https://p.dw.com/p/1BTFu
Niger Niamey Proteste AREVA Uran
Hoto: DWM. Kanta

A jamhuriyar Nijar hadaddiyar kungiyar daliban kasa baki daya wato USN ta kira magoya bayanta zuwa ga shirya wata zanga-zangar lumana a duk fadin kasar, kungiyar ta dauki wannan mataki ne a wani kokari na neman tilastwa gwamnatin kasar daukar matakan shawo kan wasu jerin matsaloli da ta ce sun dabaibaye tafiyar da harakar ilimi a kasar baki daya.


Tun da sanyin safiya ne dai daliban na jami'ar Abdulmumuni ta birnin Yamai da ma sauran kanansu na makarantun sakandare daban-daban na birnin na Yamai suka kamo titunan birnin suna gudanar da zanga-zangar da ma raira wakoki masu cike da habaici da kalaman sukar lamirin magabata, kafin daga karshe suka tare a gaban harabar majalissar dokokin kasar, inda suka gudanar da babban taron gangamin na su.

Weltmädchentag
Dalibai na begen samun illimi mai zurfiHoto: picture-alliance/dpa/Plan International

Matsalolin da daliban kasar ke fiskanta

Malam Mamud Bukari Isufu daya daga cikin shugabannin kungiyar daliban makarantun sakandare ta birnin Yamai ya bayyan mana wasu daga cikin matsalolin dake ci ma makarantun sakandaran birnin tuwo a kwarya wadanda suka yi dalilin fitowarsu a yau.

Dubban daliban jamiar Abdulmumuni ta birnin Yamai dai ne suma suka halarci wanann taron gangami, bayan sun gudanar da zanga-zangar kuma Malam Bafade Adamu Murtala mataimakin magatakardan kungiyar daliban kasar ta Nijar ya zano mana wasu daga cikin matsalolin da jami'o'in kasar ta Nijar suke fuskanta.

Daga bisani dai na tuntubi magatakardan ofishin ma'aikatar
ilimi mai zurfi wanda ya ce da mu gwamnatin ba ta manta da matsalolin daliban ba, domin kuwa tuni ta girka kwamitin da ya yi nazarin jerin bukatun daliban kimanin 65 wadanda tuni suka fahimci juna a mafi yawan ganawar da suka yi, wadanda kuma yake sa ran za su kai ga cimma yarjejeniya nan ba da jimawa ba.

Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Pinado Abdu Waba