1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar kare demokaradiyya a Nijar

Issoufou MamaneDecember 21, 2015

'Yan siyasa masu goyon bayan gwamnati a Nijar, sun gudanar da zanga-zanga a birnin Tahoua da ke Arewacin kasar domin yin Allah wadai ga yunkunrin juyin mulki.

https://p.dw.com/p/1HRE5
Hoto: DW/L. Hami

A wannan Litinin din ce, jam'iyyun siyasa na kawancen da ke mulki a kasar suka kira wani jerin gwano a birnin Tahoua wanda ya hada 'yan siyasa da kungiyoyin fararan fulla, da na dalibbai, da ma 'yan kasuwa domin nuna kyama ga abun da su ka kira yunkurin yiwa demokaradiyya zagon kasa a Nijar bayan yunkurin juyin milkin da gwamnati ta ce ta gano a kasar a makon jiya. Masu jerin gwanon sun nuna goyon bayansu ga jami'an tsaro da gwamnatin Shugaba Issoufou Mahamadou tare da ba su kwarin gwiwa kan harkokin tafiyar da ayyukansu na mulki. Gwamnan jihar ta Tahoua, Alhaji Barmu Salifu, ya nuna gamsuwarsa ga masu jerin gwanon:

" Wannan babbar rana ce garemu al'ummar jihar Tahoua kuma ina farin ciki da sunan Shugaban kasa Alhaji Issoufou Mahamadou da gwamnatinsa, ina mika muku godiya ta ga wannan taro da kuka yi na nuna goyon bayanku ga shugaban kasa."

Niger - Demonstration gegen den Terror in Zinder
Hoto: DW/L. Hami

A lokacin da ya ke magana gaban dubban jama'a, shugaban zauren shawara na da'irar birnin Tahoua, Alhaji Abdoura'ouf Dodo shi kuma takaicinsa ya nuna ga yunkurin juyin mulkin, inda ya ce lokaci ya wuce na juyin milki domin demokaradiyya ta zauna yanzu a Nijar. Shi dai, wannan jerin gwanon ya samu halartar rukuni da dama na al'umma ciki kuwa har da 'yan farar fulla da 'yan kasuwa, da dalibai inda ga baki dayansu suka nuna rishin goyon bayan abun da suka kira yunkurin mayar da hannun agogo baya.

Niger Niamey Proteste AREVA Uran
Hoto: DWM. Kanta

To sai dai 'yan adawa ba su halarci jerin gwanon da aka yi ba, inda a cewar daya daga cikin 'yan adawar basu halarta ba domin ana cikin yanayi na bincike kuma batu ne da ke a hannun shari'a wadda ita ce za ta tabbatar ko abun da ake zargin sojojin da yi gaskiya ne ko akasin haka. Sai dai kuma 'yan adawar sun yi fatan Allah ya tona assirin duk wani mai shirya mugun nufi ga kasar ta Nijar. Masu zanga-zangar dai sun yi ta rera wakokin nuna kishin kasa yayin wannan jerin gwano na birnin Tahoua.