1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin Almundahana a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou
April 26, 2017

A Jamhuriyar Nijar zargin karkata Sefa miliyan dubu dari biyu da ake yi wa tsohon daraktan fadar shugaban kasa Hassoumi Massaoudou ya kara zafi. 'Yan adawa a majalisa sun bayyana sakamakon binciken da suka yi.

https://p.dw.com/p/2bxgf
Gebäude der Nationalversammlung in Niamey Niger
Hoto: DW

Su dai 'yan bangaren na adawa na fatar ganin majalisar ta dokoki a kasar ta tube rigar kariyar tsohon daraktan fadar shugaban kasar ne don yi masa shari 'a saboda ganin gaskiya ta yi aikinta. Tun daga farko dai a wannan Larabar ce ta kamata kwamitin binciken da majalisar dokoki ta kafa mai manbobi 10, biyu 'yan adawa ya bayyana a gaban majalisar domin gabatar da rahotonsa wanda majalisar ta dorawa nauyin zakulo kudade Sefa miliyan dubu 200 da ake ce-ce-ku-cen cewar tsohon daraktan Fadar shugaban kasa Hassoumi Masaoudou ya batar, biyo bayan kafa kwamitin a 17 ga watan jiya,

Sai dai bayyanar manbobin kwamitin ke da wuya a majalisar daukacin yan adawar suka kauracewa tare da cewar basu aminta da sakamakon binciken rahotonba saboda tattare yake da rashin gaskiya tantagaryarta. Hasali ma 'yan adawar sun wallafa nasu rahoton da suka ce shine na gaskiya don al'ummar kasar ta sani, To ko mi takamaimain binciken na yan adawa ya tabbatar ? Onorabul Soumana Sanda, Kakakin 'yan adawa ne a majalisar dokoki.

Ya ce ''binciken ya nuna abubuwa da yawa, ya 'yan jarida suka fadi ya zama gaskiya tunda da aka kira shi bai musa ya sa hannu a kan takardun da suka salwantar da kudaden ba. Ya yi abubuwa da dama ba bisa ka'ida ba kuma mu a yanzu a matsayin mu na 'yan majalisa babu wata hanyar da zamu bi gaskiya ta fita munyi kokarinmu'' 

Ina mafita?
'Yan adawar sun ce a yanzu hanya mafi a'ala game da badakalar ita ce na bari kotu ta yi aikinta ta hanyar gurfanar da Hassoumi Masaoudou a gaban shari'a inda kuma 'yan adawar suka ce sun sanya kira ga majalisar dokoki da ta tube masa rigar kariya.

Sai dai da take mayar da martani game da wannan bukatar ta 'yan Adawa, jam'yyar PNDS Tarayya ta bakin dan majalisar dokoki Onorabul Iro Sani ta ce:

Sitzung des Parlaments in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

''Zargin baya da tushe ballantana makama. Hasalima da 'yan adawar na da gaskiya da kamata yayi su tsaya a tabka mahawara a zauren majalisa. Yadda 'yan jarida suka wallafa wannan labarin na karya haka su ma rahoton na su yake na karya. Sun gaza tsayawa a yi muhawara. Da ma ba su da aiki sai su shige daka, duk abin da suke yi mun sani; su shiga su fita mun sani sarai kifi na ganinka mai jar koma. Wai tsige Masaoudou, to su je su tsige ga shi can basu isa ba su nyi kadan''

Yanzu hakan dai hankali ya karkata ne kan yadda za ta kaya a majalisar tsakanin 'yan adawar da suka ambaci wannan bukatar da kuma bangaren masu rinjaye, ganin cewar ko a ranar 3 ga watan Maris ma gabanin kafa wannan kwamitin binciken da ya haifar da wannan ce-ce-ku-ce, 'yan adawar suka bukaci kafa shi kuma bangaren masu rinjaye ya nuna amincewarsa. Wannan dai shi ne bangare na uku da ke bukatar Hassoumi Massaoudou ya gurfana gaban Kotu don wanke kansa daga zargin karkata wadannan makudan kudaden.