1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin satan agajin 'yan gudun hijira

Al-Amin Suleiman Muhammed/USUAugust 9, 2016

Ana zargin karkatar da manyan motocin dakon kayan abinci 60 da Gwamnatin Tarayyar ta ware domin tallafawa al’ummmar jihar Borno da ke fiskantar matsalar yunwa

https://p.dw.com/p/1Jerp
Niger Binnenflüchtlinge Flüchtlinge Vertriebene Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/Stringer

A watan Afrilun da ya gabata ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umurnin tura ton dubu goma na hatsi ga Jihohin shida na shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya, domin rage musu radadin da suke ciki sanadiyyar rikicin Boko Haram. To sai dai daga cikin wadanda aka tura Jihar Borno wacce ita ce ta fi fama da rikicin an kai tireloli hamsin ne kawai, inda ake zargin karkatar da man'yan motocin kayan abincin guda 60 daga cikin 113.

Sanata Ali Ndume Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriya wanda dan asalin jihar Borno ne, ya ce abin takaici ne ganin yadda aka karkatar da wannan kayan abinci da aka shiya kaiwa marasa karfi, don rage tsananin da al’umma ke fama da shi na yaki da Boko Haram kuma hakan rashin imani ne.

Sanata Ndume ya nemi sauran masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kan su da su sanya hannu cikin aiki agajin wadan nan bayin Allah. Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da dubban ‘yan gudun hijira a jihar Borno ke bayyana mummunan hali da suka samu kan su a ciki. Kamar yadda wasu daga cikin suka shida wa DW, a wata ziyara da wakilinmu Al-Amin Muhammad ya kai a wasu sansanonin ‘yan gudun hijirar a Maiduguri.

Kashim Shettima Gouverneur Bono Nigeria
Kashim Shettima, Gwamnan jihar BornoHoto: DW/U. Shehu

Yanzu haka dai jama’a na ci gaba da bayyana damuwa kan halin da wadan nan ‘yan hijira ke ciki, inda suka bukaci agajin gaggawa na musamman daga gwamnatin Tarayyar Najeriya, don ceto rayukan al’umma da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunun su. A cewar Alhaji Ali Bolori wani mazaunin Maiduguri da ke bayyana damuwa kan halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki.

DW ta yi nemi jin tabakin hukumomin da ke kula da ‘yan gudun hijira, amma kokarin na ya ci tura. Sai dai a baya gwamnatin jihar Borno da ma hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, sun ce suna bakin kokarin su wajen ganin an rage wahalhalun da ‘yan gudun hijirar ke ciki musamman samar musu da abinci da magunguna da kuma wararen da za su tsuguna.