1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zuma na kan gaba a zaben Afirka ta Kudu

May 8, 2014

A lokacin da hukumar zaben Afirka ta Kudu ke tantance kuri'un da aka kada a zaben gama gari, akaluma sun nunar da cewa jam'iyyar ANC ta yi wa DA rata da yawan kuri'u.

https://p.dw.com/p/1Bvsu
Hoto: picture-alliance/dpa

Kashi daya bisa uku na yawan kuri'un da aka kada ne hukumar zaben Afirka ta Kudu ta yi nasarar tantancewa ya zuwa. Sai dai kuma tuni sakamakon farko ya nunar da cewar jam'iyyar ANC ta lashe kashi kusan 60 daga kuri'un da aka kada. Da ma dai masu lura da al'amuran siyasa a Afirka ta Kudu sun riga sun yi hasashen cewa jam'iyyar ta marigayi Nelson Mandela za ta kai labari a wannan zabe. Ko da kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar sai da ta nunar da cewa jam'iyyar ANC za ta iya lashe kashi 65 daga cikin 100 na daukcin kuri'un da aka kada.

Idan ko wannan hasashe ya tabbata, to dai shugaba da ke ci a yanzu wato Jacob Zuma zai samu damar yin tazarce sakamakon rinjaye da jam'iyyarsa ta ANC za ta samu a majalisa. Hasali ma dai jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance ta na biya mata baya ne da kashi 27 daga cikin 100 na kuri'un da aka kada. Alhali ta yi alkawari ba wa marada kunya, musamman ma bayan da farin jinin Zuma ya ragu sakamakon amfani da kudin kasa da ya yi wajen kwaskware gidansa.

Südafrika Wahlen Wahllokal 07.05.2014
'Yan Afirka ta Kudu sun yi tururuwa a runfunan zabeHoto: Reuters

ANC za ta canja kamun ludayinta

Tuni dai jam'iyyar ANC ta yi alkawarin canja kamun ludayinta a wa'adinta na gaba, a inda za ta yi tsayuwar daka don ganin cewa ta inganta harkokin ilimi da na kiwon lafiya. Hakazalika ta ce za ta sa kafar wando guda da miyagun laifuffuka, tare da cike gibin da ke tsakanin masu hannu da shuni na kasar da kuma 'yan rabbana ka wadatamu. Da ma dai bakaken fata na Afirka ta Kudu sun nuna bacin ransu dangane da rashin cika alkwarinta da gwamnati ba ta yi na sake mallaka musu filayen noma.

Wannan dai shi ne karon farko da 'Yan Afirka ta Kudu da aka haifa bayan da aka kawar da akidar wariyar launin fata shekaru 20 ke nan da suka gabata suka kada kuri'a. Sai dai kuma ba za a san hakikanin wanda ya lashe zaben gama-gari na Afirka ta Kudun ba sai idan hukumar zabe ta bayyana cikakken sakamakon a ranar Alhamis mai zuwa.

Wahlkampf aus Südafrika von Julius Malema
Julius Malema bei Kai labari ba a zaben gama gariHoto: picture-alliance/dpa

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Mawallafi: Usman Shehu Usman