1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alamun rashin hada karfi kan yaki da Boko Haram

Amin Suleiman MohammadMarch 4, 2015

Masana tsaro sun bayyana fargabar cewa rashin hadin kai tsakanin Najeriya da Chadi da Nijar gami da Kameru na zama barazana ga shirin da ake yi na kafa runduna daya da za ta tunkari Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1El6D
Tschad Armee Boko Haram
Hoto: Reuters/E. Braun

Sama da Sojoji dubu takwas ne kasashen da ke bakin gabar tabkin Chadi wato Najeriya da Kamaru da Jamhuriyar Nijar da kuma Chadi suka amince su samar domin tunkarar mayakan kungiyar Boko Haram da ke zama babbar barazana ga daukacin kasashen.

Sai dai ya zuwa yanzu kasashen ba su kafa runduna daya tilo da za ta tunkari wannan fada da kungiyar Jama'atu Ahlul Sunna Li'Dawati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ba.

Goodluck Jonathan im Boko Haram Gebiet Baga
Hoto: picture-alliance/dpa

Yanzu haka dai dukkanin kasashen na yin gaban kansu ne a wannan yaki inda yawanci suke kare yankunan iyakokin da kuma wuraren da suke iko sabanin yadda a baya ake ganin za su hadu domin tunkarar yakin tare.

Kasashen na kai farmakin soji ne ba tare da haduwa da sauran sojojin kasashen da aka yi hadakar da su ba abin da masana ke ganin na barazana ga kokarin samun nasarar wannan yaki.

Daukacin kasashen dai na nuna irin nasarorin da kowace kasa take samu tare da nuna wa manema labarai abin da ke kara tabbatar da irin yadda suke yin yakin ba tare da hada kai da sauran kasashen da aka yi yarjejeniya da su ba.

Rahotanni sun bayyana cewa sojojin Chadi sun yi zargin cewa an katse hanzarin su na ci gaba da kutsawa cikin wasu sassan Najeriya bayan da suka samu nasarar kwato garuruwan Malumfatori da Dikwa duk a sassan Najeriya.

A cewarsu an dakatar da su daga yin gaba domin karbo wuraren da Boko Haram ta kame a cikin Najeriya duk da nasarorin da aka ga sun samu a cikin kankanin lokaci.

Kamerun Flüchtlingslager Minawao
Hoto: AFP/Getty Images/R. Kaze

Najeriya da ke zama uwa ma ba da mama dai ta ki cewa komai kan wannan batu na rashin hadin kai inda kuma ta musanta duk wani zargin na aikata ba dai dai ba a wannan yaki da take fatan kawo karshen san an makonni uku wato kafin zabukan kasa baki daya a karshen wata na Maris.