1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hama Amadou na ci gaba da zaman gidan kaso a Fillingue

Mahaman KantaDecember 9, 2015

Kotun kolin Jamhuriyar Nijar ta sanar a wannan Laraba 09 ga watan Disamba cewa bata da hurumin bada izinin sakin talala ga Hama Amadou tsofon kakakin majalisar dokokin kasar.

https://p.dw.com/p/1HJpa
Hama Amadou
Hama AmadouHoto: DW/S. Boukari

Da safiyar wannan Laraba ce dai kotun kolin karya shari'a wato "Cour de Cassation" ta yi watsi da bukatar yi wa Hama Amadou, tsohon kakakin Majalisar dokoki kasar Nijar, kuma shugaban jam'iyar Moden FA Lumana Afirka, da ke cikin kawancen jam'iyyun adawa sakin talala. Hama Amadou na tsare ne a gidan kason garin Filingué da ke a nisan km sama da 100 da birnin Yamai tun ranar 14 ga watan Nowumba da ya gabata, ranar da ya dawo daga gudun hijirar da ya yi ta kusan shekara guda a birnin Paris na kasar Faransa, bayan da ya zargin hukumomin kasar da amfani da batun zargin da ake masa na hada baki da matarsa wajan sayan jarirrai domin hallakashi.

Hama Amadou, Parlamentspräsident in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Kan wannan batu dai na zargin sayan jarirrai, a baya an gurfanar da mutane da dama kafin daga bisani katu ta yi mu su sakin talala cikin su kuwa har da tsofon Ministan noma Abdou Labo wanda yanzu haka jam'iyyarsa ta CDS Rahama ta sayar da shi a matsayin dan dakararta a zaben shugaban kasa mai zuwa. Hama Amadou dai ya sha musanta wannan zargi da ake yi masa na safarar jarirrai, inda ya ce zargin na da nasaba ne da siyasa. A ranar 2 ga wannan watan nan ne dai lauyoyin da ke kare shi suka ajiye takardar neman a yi ma sa sakin talala. A halin yanzu dai babbar ayar tambayar ita ce ko wane alkali ne kuma ke da hurumin bada belin ga shugaban jam'iyyar ta Lumana Afirka Hama Amadou da ake yi wa kallon babban mai adawa da manufofin shugaban kasar na Jamhuriyar Nijar Issoufou Mahamadou.