1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Rikicin cikin gida a APC

February 4, 2022

Rikici cikin gida a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya na kara kamari, inda aka rantsar da shugabannin jam'iyyar na jihohi cikin rikici da turjiyar 'ya'yan jam'iyyar a jihohi dabam-dabam.

https://p.dw.com/p/46Xkd
Najeriya APC
Kalubale ga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya gabanin zaben 2023Hoto: DW/K. Gänsler

A jihohin kamar su Kwara da Osun da kuma Kebbi dai, wasu 'ya'yan jam'iyyar sun nuna rashin dadinsu da kuma kin amincewa da shugabannin da aka rantsar. Duk da share tsawon lokaci ana kai kawo a kokarin sulhu dai, APC ta kare tare da tabbatar da tasirin gwamnoni a kan ikon jam'iyyar. Gwamnonin ne dai suka tabbatar da samun nasu a daukacin mukaman shugabancin na jihohin jam'iyyar, a wani abun da ake shirin gani wajen zaben fitar da gwanin jan ragamar jam'iyyar a zabukan badi. 

Karin Bayani: Rikicin jam'iyyar APC na kara ta'azzara

Wannan batu dai na shirin bata ran da dama na masu tsintsiyar da ke karatun adalci, amma kuma ke kallon baki da rodi-rodi a yanzu. APC dai ta yi nasarar rantsar da daukacin shugabannin jam'iyyar a matakai na jihohin kasar, in ban da jihohin Kano da Sakkwato. To sai dai kuma daga dukkan almu rai na bace, kuma hankalin 'ya'yan jam'iyyar ya tashi a jihohin kasar dabam-dabam. Hon Shehu Haruna Lambu dai na zaman jigon APC a Kano, kuma cewarsa ana bukatar taka tsan-tsan da nufin kaucewa jefa jam'iyyar a cikin rudani.

Yakin neman zabe na jam'iyya APC a Kano
Gwamnan Kano Abdullahi Umar GandujeHoto: Salihi Tanko Yakasai

To sai dai koma zuwa ina Abdullahi Umar Ganduje da ke zaman gwamna daya tilo da uwar jam'iyyar ta kasa sanya kafa ta shure zaben da ya yi na shugaban jam'iyyar ta APC a jiharsa ta Kano, ke shirin zuwa da magoya bayansa, can ma a jihar Kebbi dai wasoson gwamnan ga dukkan alamu bai yi wa Sanata Adamu Alero da ke zaman daya cikin jagororin jam'iyyar dadi ba. Ko ma ya take shiri da ta kaya ya zuwa babban taron jam'iyyar na kasa dai, akwai tsoron rikidewar rikicin ya zuwa fashewar APC.

Karin Bayani: Hanyoyin sasanta rikicin jam'iyyar APC

Irin wannan rikici ne dai ga misali, ya kai ga fara lalacewar lamura a cikin PDP da ta kalli ficewar 'ya'yanta zuwa ga adawa a shekara ta 2014. To sai dai kuma a tunanin Faruk BB Faruk da ke sharhi kan batun na siyasa, har yanzu masu tsintsiyar da ke kan mulki suna da sauran dama kafin kai wa ga takara ta zabe na gari. A karshen watan da muke ciki ne dai, masu tsintsiyar ke shirin su dora tare da zabar shugaban da zai ja ragamar jam'iyyar ya zuwa babban zaben.