Kalubalen da ke gaban sabon shugaban Mali
September 19, 2013Talla
Mali wadda ta shafe shekaru masu yawa tana zaman abar koyi ga sauran kasashen Afirka ta Yamma, to amma juyin mulkin da sojoji suka yi da kuma yakin basasan da ya biyo baya, sun gurgunta al'amura a kasar musamman a yankin arewa, inda har yanzu ake kokarin wanzar da zaman lafiya.